Halayen Imam Ali a.s



Ayyukansa (a.s) a wajen yada daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awa sun kasance tare da gaba dayan kwanakin rayuwarsa daga farkonta har ya zuwa karshenta.

Daga cikin ayyukansa mafi shahara akwai:

1. Kwanansa a kan shimfidar Annabi (s.a.w) domin ya fanshi Annabi (s.a.w) daga kisan gillar da mushirikan Kuraishawa suka shirya.

2. Jagorantar tawagar masu yin hijira daga Makka zuwa Madina.

3. Jarumtakarsa a cikin yakokin Musulunci mafi shahara kamar: Badar, da Uhud, da Khandak, da Hunain, da Khaibar, da kuma yakin Bude Makka.

Halifancin Imam Ali (a.s) ya kasance ne bayan rasuwar Annabi (s.a.w) nan take (ba tare da wata tazara ba), hakan kuwa a saboda dalilai masu zuwa:

1. Saboda Nassosi a fili wadanda Annabi (s.a.w) a cikinsu yake nuna khalifa bayansa, kuma yake karfafa halifancin nasa a cikinsu.

Kuma daga cikin Nassosi mafi shahara: Hudubarsa (s.a.w) a Ranar Gadir a lokacin dawowarsa daga hajjin bankwana.

Kuma saboda Imam Ali (a.s) shi ne ya fi Musulmai dacewa da daukan nauyin halifanci bayan Annabi (s.a.w), saboda samun sharudda guda biyu na Imamanci a tare da shi.

Shi dai ya kasance Maط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢asumi ne, saboda dalilai masu zuwa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next