Halayen Imam Ali a.s



Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza. (Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100). Wani hadisin ya zo cewa: Jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki, da lamunce rayuwa, da adalci.

Musulunci ya zo da tsarin da ba shi da misali: ya haramta, ya wajabta, ya kwadaitar, ya karhanta, ya halatta. Duba abubuwan da aka wajabta a musulunci guda: 115, da kuma wadanda aka haramta guda: 97, da wasu: 112, da munanan halaye guda: 95, da kuma kyawawan halaye: 83, a littafin Tafarkin Rabauta.

Duk da yakin da daular Imam Ali (a.s) ta sha na kawo mata hari daga munafukai da makiya Allah da manzonsa (s.a.w) amma wannan bai hana samar da walwala da yalwata wa mutane ba, kuma yaki bai shagaltar da Imam Ali (a.s) daga maganin talauci da fatara daga alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma ba, kuma bai hana shi aiwatar da adalci ba, bai hana shi ilmantar da mutane ba, bai hana shi dukkan wani abu da daular da ta fi kowacce zaman lafiya take yi ba!.

Imam Ali (a.s) shi ne ya fi kowane mutum jaruntaka a fagen fama kuma wannan lamari ne da ya shahara daga gareshi, ya kasance ya fi kowane mutum a duniya zuhudu bayan annabi (s.a.w), yana gyara takalminsa da kansa, yana dinke tufafinsa, yana gyara tsakanin mutane, yana ganin duniya ba ta kai kimar ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¹آ©yar majina da akuya take fyatowa daga hancinta ba, kimar duniya a wurinsa shi ne tsayar da umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, da tsayar da hukuncin Allah madaukaki.

Imam Ali (a.s) ya shahara da yin tsanani kan hakkokin mutane har sai ya kwata daga hannun azzalumai ya mayar da shi ga masu shi, ya kasance yana tsananta  wa gwamnoninsa da wakilansa kan alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢amuran mutane, yana yi musu hisabi mai tsanani kan dukiya da amana da hakkokin mutane na jini da na dukiya da mutunci.

Wasu mutane suna ganin idan sun yi umarni da kyakkyawa ko hani daga yin mummuna to wannan zai hana su wani arziki, ko ya kai ga jefa su cikin kunci, ko ma kisa, amma Imam Ali (a.s) yana ganin sabanin hakan, yana ganin cewa; umarni da kyakkyawa ko hani daga mummuna ba sa hana mutum arziki, kuma ba sa kusanto da azalinsa.

Imam Ali (a.s) shi ne shugaban masu hikima da ilimi, kuma littafin da ya tattaro bayanai game da hudubobinsa da hikimominsa, da wasikunsa sheda kan hakan. Ya kasance makoma ga dukkan sahabbai wurin sanin abin da suka jahilta bayan wucewar manzon rahama (s.a.w), sannan kuma ayoyi sama da 300 ne suka sauka game da falalarsa kamar yadda Ibn Abbas yake tabbatar da hakan. Sannan hatta da makiyansa kamar su Muط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awiya da Amru dan Asi sun yi masa sheda da babu kamarsa.

Idan zai zabi wanda zai kasance gwamnansa ko wakilinsa yana zaba daga mutane ne masu hankali da takawa da ilimi, bai taba zaba don son mutum ba ba tare da ya cancanta ba.

Tarihin Imam Ali (a.s) shi ne Ali dan Abu Dalib (a.s) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Asad (a.s) shi dan ammin Manzon Allah ne kuma mijin 'yarsa kuma wasiyyinsa halifansa a kan mutane bayansa wato; Amirul muminin mahaifin imamai (a.s).

An haife shi a Ka'aba mai girma a Makka ranar juma'a daren sha uku ga watan Rajab bayan shekaru talatin da haihuwar Annabi (s.a.w) kuma ya yi shahada daren juma'a a masallacin Kufa a mihrabi da takobin ibn muljam muradi ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ“daga cikin hawarijawa- wannan kuwa a daren sha tara ga watan Ramadan ne kuma bayan nan da kwana uku ne a daren ishirin da daya na Ramadan ya yi wafati yana da shekaru sittin da uku, Imam Hasan da Husain (a.s) sun shirya janazarsa kuma suka binne shi a Najaf inda kabarinsa yake yanzu da wasiyyarsa (a.s) domin ya kubuta daga sharrin hawarijawa da Hajjaj daga tone kabarinsa, kuma wannan ya amfane shi[5], kuma Imam Ja'afar Sadik da Imam Musa Kazim (a.s) su ne suka nuna wa mutane inda kabarinsa yake (a.s).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next