Halayen Imam Ali a.sAmma a siyasar Imam Ali (a.s) ta karbar haraji muna ganin yadda yake gaya wa Malik Ashtar kan cewa: "Dubanka wurin gyaran kasa ya fi yawa kan dubanka kan karbar haraji, domin ba a samun wannan sai da gyara kasa, kuma duk wanda ya nemi haraji ba tare da gyaran kasa ba to ya rusa kasa, kuma ya halaka bayi, kuma lamarinsa ba zai wanzu ba sai kadan". Sai ya yi nuni da cewa karbara haraji ba tare da gyara kasa ba yana daga cikin abin da yake rusa kasa gaba daya. Wannan lamarin ya sanya masu kin gaskiya kyaram wannan hukumar adalci ta Imam Ali (a.s), suka yi kokarin ganin gaba da ita ta kowane hali. Game da lamarin tafiyar da lamurran al'umma kuwa Imam Ali (a.s) ya yi siyasar daidaito tsakanin kowane mutum ba tare da nuna bambancin matsayi ko kabila ko waninsu ba, ya daidaita mutanen ta fuskancin: 1. Hakkokin wajibi 2. Kyauta da baiwa 3. Dokokin kasa Sannan ya tilasta gwamnonisa yin hakan a tsakanin al'ummarsa, yana mai duba lamurransu domin kada su kauce wa hanya. Sannan Imam Ali (a.s) bai taba tilasta mutane Don haka ne zamu ga hatta da abokan hamayya Imam Ali (a.s) bai taba hana su nasu 'yancin fadin ra'ayinsu ba, ya sakarwa kowanne 'yancin fadin albarkacin bakinsa, hatta da hawarijawa ya ba su 'yancin komai har na neman ilimi da aminci bai dauki mataki kansu ba duk da abin da suka yi har sai da suka far wa al'ummar musulmi da kisa sannan sai ya dauki mataki kansu domin magnain barnarsu a cikin al'umma, da kariya ga al'umma daga sharrinsu domin sanya aminci cikin al'umma. Ba a samu wani mutm da ya kai kiran mutane zuwa ga hadin kai ba tun bayan manzon Allah (s.a.w) ba kamar Imam Ali (a.s), ya yi matukar kokarin ganin ya samu dinke barakar al'ummar musulmi sai dai munafukai sun yi kokarin ganin rarraba ta matukar gaske, hatta da munafukai irin su AbuSufyan da suka nemi taimaka masa da makamai da dawakai domin ya karbi hakkinsa na jagoranci daga hannun Abubakar sai ya ki yarda domin gudun kada al'umma ta fada cikin yaki, sannan kuma ya gane cewa hadafin munafukai shi ne tarwatsa musulunci. Don haka ne ya ce masa:
|