Halayen Imam Ali a.s



3. Dawo da gaba dayan abin da aka karba na dukiya a bisa tsarin rabo wanda aka kirkira.

4. Yin fada da kungiyoyi azzalumai wadanda suka soke shi a kan aikata tsarin Musulunci wanda ya yi a yakokin: Basara, da Siffin, da Nahrawan.

Imam Ali (a.s) ya rasu a cikin watan ramadhan shekara ta (40 bayan hijira) mutuwar kisan gilla a sakamakon zartar da shirin khawarijawa: wanda yake nufin kawo karshen shugabannin masu yin fada da khawarijawa.

Daga cikin shiryarwarsa: Ku sani bayin Allah (s.w.t) cewa fa shi mumini a wannan shekarar yana halatta abin da ya halatta a shekarar farko. Kuma a wannan shekarar yana haramta abin da ya haramta a shekarar farko. Kuma ku sani fa cewa mutumin da ya fi kowa haifar da bakin abubuwa ba zai halatta muku wani abu ba daga cikin abin da aka haramta muku. Shi dai halal shi ne abin da Allah ya halatta. Kuma haram shi ne abin da Allah ya haramta. Hakika kun gwada alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢amura, kuma kun waط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢azantu da wadanda suka kasance kafinku. Sannan an buga muku misalai, kuma an kiraye ku zuwa ga alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢amari bayyananne. Don haka babu mai rufe kunnensa daga hakan sai kurma, kuma babu mai rufe Idonsa daga hakan sai Makaho. Kuma duk wanda Allah bai amfanar da shi ba ta hanyar balaط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢i da tajrubobi, to bai amfana da wani abu daga cikin waط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢azi ba. Kuma takaitawa ta zo masa, har sai ya san abin da ya musa, kuma ya musa abin da ya sani. Su dai mutane guda biyu ne: mai bin tafarkin gaskiya da mai bin tafarkin bata babu wani dalili na Sunna daga Allah a tare da shi, kuma babu hasken wata hujja.

Kuma Allah (s.w.t) bai yi wa wani waط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢azi ba da, makamancin wannan Kur'anin domin shi igiyar Allah ne mai kwari, dalilinsa ne amintacce, kuma a cikinsa ne tsayuwar zuciya wajen tunani take, da kuma mabubbugar Ilimi. Kuma zuciya ba ta da abin da yake tafiyar mata da bakin ciki da kokwanto ban da shi. Duk da cewar masu waط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢azantuwa sun riga sun wuce sai masu mantuwa ne suka rage.

Don haka idan kuka ga abin alheri to ku taimaka a kan sa. Kuma idan kuka ga wani abin sharri to ku kauce masa.

Nahjul Balaga: Shi dai tarin hudubobi ne masu Kayatarwa na Imam Amirul muط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢uminina (a.s) da wasiyyoyinsa da wasikunsa da kuma gajerun kalmominsa na hikima.

Wanda ya tattara shi: Sayyid ash-sharif arradhi daga cikin malamai da masana adabi na karni na hudu bayan hijira.

Usulubinsa: Nahajul balaga bayan Kurط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ani da maganganun Annabi (s.a.w) kyawawa, sai shi a wajen daukakar usulubinsa na adabi. Ya fifita da zurfin tunani, da gaskiyar badini, da kayen bayaniط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¢آ¦ da adon zance, da kyawun maط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ana, da jan hankalin magana, da kuma babban tasiri ga mai karatu da mai sauraro.

Nahjul balaga ana kirga shi daga cikin muhimman littattafanmu manya wadanda suke a hannunmu a yanzu. Kuma ana fito da muhimmancinsa da abubuwa masu zuwa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next