Halayen Imam Ali a.s



ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¥â€œRinin Allah waye ya fi Allah iya rini, kuma mu masu bauta ne gareshiط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ’ (Bakara: 138). Sai Allah ya runa su da shiriyarsa da rahamarsa, sai suka runa mu da shiriyar da Allah ya yi musu, don haka ne Muhammad (s.a.w) ya kasance rahamar Allah ga talikai baki daya, a bayansa kuma Littafin Allah da Alayensa (a.s).

Sai aka wajabta salati gareshi tare da wadannan Alayen nasa goma sha uku, sai aka yi masa niط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢imomi da babu wanda ya same su. Mataki ne na ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¥â€œHamdط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ’, da wajabcin yi masa salati. Da wasu niط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢imomi kuma da babu mai samun su sai ya roka kamar yadda aka yalwata masa kirjinsa, aka sanya masa Ali danط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢uwansa wasiyyinsa mai karfafarsa.

Babu wani addini da ya zo da rahama ga alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma fiye da wannan addini na karshe, domin wanda aka aiko da shi yana dauke da rahamar Allah (s.w.t) tare da shi. Don haka ne ma ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¥â€œ... Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai...ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ’ (Anbiya: 107). Da wannan ne zamu ga addinin nan madaukaki na musulunci ya zo da lamunin rayuwar dukkan dan Adam wacce ba ta kebanta da musulmi ba. Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da daukar nauyin al'amuran al'umma da zamu kawo wasu kamar hakan:

Daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta da shi bayana". Sai aka ce da shi Imam Ja'afar Sadik me wannan yake nufi? Sai ya ce: Fadin Annabi (s.a.w) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce"(Tafsiri Nurus sakalain: mujalladi 4, shafi: 240).

A wata ruwaya ta Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kubuta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi"[2].

Bayan Imam Sadik ya fadi wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: "Babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (s.a.w), kuma sun yi imani da su da iyalansu"[3].

A wata ruwayar Sheikh Mufid ya karbo daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "Ya ku jama'ar musulmi! Ni an aiko ni ne kusa da alkiyama ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¢آ¦ -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to ta iyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni"[4].

Haka nan ya karbo daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karba kuma bai ciyar da ita a barna ko sabo ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka duk abin da yake kan Annabi (s.a.w), yana kan jagora. (Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 492).

Da wdannan dokokin da ire-irensu masu yawa musulunci ya sanya talauci ya kawu daga dukkan daular da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya a wancan zamanin. Talauci ya kawu ta yadda kusan idan ka ga mai roko to zai kasance abin mamaki, musulunci ba ya son zama cikin kaskancin rokon mutane, don haka ne ya kawar da talauci, ya sanya dokokin lamunin rayuwar alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma. Duba mamakin da Imam Ali ya yi yayin da ya ga wani yana bara a kwararon birinin Kufa.

Hurrul Amuli kuwa ya ambaci cewa: Imam Ali (a.s) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa Mene ne haka? Sai ya ce: Ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara. Sai Imam Ali (a.s) ya yi fushi ya ce: Kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rika rayuwa da shi (Wasa'ilus Shi'a).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next