Zabar Mace Ko Namijin Aure



3- Rasa gani da makancewa daga karshe;

4- Karkarwar jiki;

5- Rashin nutsuwa;

6- Yawan tunani;

7- Son warewa waje daya, shi kadai;

Wasiyyoyi Domin Maganin Istimna’i

Malamai sun kawo wasu abubuwa da suke maganin wannan mummunan ciwo mai haifar da miyagun halaye da munanan dabi’u kamar haka:

1- Nisantar duk wani abu mai kawo sha’awa, kamar kallon fila-falai da mata suke rawa ko suke sanya kayan da bai dace ba, da duk abin da ya san yana sanya shi jin sha’awa.

2- Shagaltar da kansa da wasu abubuwan, kamar tsara lokutansa, na karatu da na zuwa filin wasa, ya kuma rika yin wasan motsa jiki, da karanta littattafai kamar na ilimi ko jaridu, da zuwa wajan hutawa da shakatawa domin ya samu saukin kuncin ransa, da ware lokacin da zai rika yin yawace-yawace a lokacin da ba shi da komai, da yawan karanta kur’ani koda fatiha ce a kan hanyarsa, da zuwan wajen tarurrukan wa’azi da shirya irinsu, da yawaitar zuwa masallaci a lokacin kowace salla.

3- Sanya wa kansa ayyukan da zasu cike lokacin hutawarsa.

3- Kula da wasannin motsa jiki kamar gudu a filin wasa, da daga abubuwa masu nauyi da sauransu;



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next