Zabar Mace Ko Namijin AureYa kamata kai kuma ka ji tsoron azaba ta Allah, domin sabo ba ya zama uzuri don matakar ba ta iya jan hankalin ka, ka yi kokarin ganin gyaranta mana, ka shawarci masana, da likitoci, da malamai masana kan zamantakewar iyali, sayo mata kayan ado na shafawa[39], da na sanyawa, da duk wani abu da kake bukatar ta yi maka ado, ko ta ja hankalinka da shi, sannan kuma ka sanar da ita duk abin da yake na tunani da zai taimaka mata don ta san yadda zata ja hankalinka zuwa gareta domin ta gyara muku Duniya da Lahira gaba daya, gidanku ya zama salihin gida mai cike da soyayya da kauna, wato ku gyara tunaninku game da ma’anar rayuwa tare da taimakekeniya domin gyara Duniya da Lahirarku. Haka nan idan mace tana da miji mai sandararren tunani game da rayuwar zaman tare to yana da kyau ta san yadda zata yi kokarin gyaransa koda ta hanyar shawarwari da masana ne. Daga cikin sandarewar tunani kawo wa mai gida matsaloli da zaran ya shiga gida ba tare da an bari ya huta ba, ko magana da shi kamar mace tana magana da wani namiji ajnabi, ko kuma ta yi masa magana kai ka ce namiji ce yake yi masa magana, ko nuna masa isa da jin kai kamar ana magana da wani azzalumi, alhalin a waje yana ganin ‘yan mata a hanya suna magana da samari da murya mai taushi, kuma kamar sa cinye su, da kuma ladabi. A irin wannan yanayi na halayen da kike nuna masa, da halin tunanin da kike jefa shi a ciki, don me ko ba zai yi tunanin duk sadda ya samu dama ya yi miki kishiya ba, ko in fasiki ne ya koma wa matan banza, idan kuwa mumini ne bai koma wa muminan zaurawa ba domin ya kulla aure na wani dan lokaci da su ko ma da’imin aure, ko ya yi tunanin yi miki kishiya da wata budurwa! Koda yake yana da kyau a sani, ba muna cewa dole ne in ka ga wani yana bin wasu matan ko kuma yana da tunanin yin wani aure matsalar matarsa ce ba, a nan muna magana kan yawancin abin da yake faruwa ne da mafi yawan abin da yake jawo irin wannan gurbacewar al’adu da dabi’u yake zama sakamakonsa ne. Da yawa irin wannan ya jawo an jefa mutane da dama cikin bala’i, rayuwarsu ta yi kunci, kuma sun fada wani mummunan hali, har wani yakan yi tunanin ya karo ta biyu sai ya fada irin wannan rashin dacewa, domin ita ma ta ki kosar da kishirwarsa ta rayuwar soyayya da kauna da yake bukata daga mace, ta haka ne wani kan shiga mawuyacin hali har ya cika uku ko hudu bai kashe kishirwar kauna da soyayya da take damunsa ko yake so a nuna masa ba. Domin na gida ba sa yi masa fari da fara’ar da yake bukata, idan bai ci sa’a ba sai su tara masa furfura a kansa, kuma nan da nan ya tsufa, domin matsalarsa farin da fara’ar yana ganin sa a waje ne, bai san cewa da ta shigo gidansa sai fari da murmushi da fara’a su kare ba. Kamar yadda irin wannan al’amari na sandarewar tunanin wasu samari, ko kuma yaudarar ‘ya mata da sukan yi saudayawa ya jefa matansu cikin kuncin rayuwa bayan kulla aure. Mu sani dukkan matsalolinmu gaba daya sun doru a kan rashin kiyaye abin da shari’a ta gindaya mana ne, tun daga farkon fara neman aure har zuwa karshen rayuwa da yanayin zaman tare, da an kiyaye shari’a sau da kafa da kiyaye hakkin juna kamar yadda ta gindaya, da sanin hakikanin abin da ta kunsa da aiwatar da shi a aikace da ba mu taba jin koda jayayya ko musu ba tsakanin ma’aurata[40]. Musulunci Bai Hana Yin Ado Ba
Daya daga cikin mas’aloli da ake fuskanta shi ne cakuda dokokin musulunci da al’adu, wani abin mamaki irin wannan sandararren tunani ya karu har a gun wasu da ake ganin kamar sun san wani abu na addini, amma saudayawa idan ka tattauna da su sai ka samu sun ba wa al’adun da suka taso cikinsu rigar musulunci ne, don haka sai suka rika bayar da tunani mummuna ga al’umma ko kuma suka rika kallon abin da yake al’adu shi ne musulunci. Musulunci ba sandararren tunani ba ne da ya haramta adon Allah ga dan Adam, addini ne mai tafiya da kowane waje da zamani, koda yake kada mu manta cewa wannan ta wani bangaren yana da tasiri da nau’in mazhaba wani lokaci. Amma mazhabin Ahlul Bait (A.S) da Manzo ya bar mana su a matsayin makoma bayansa, mazhabi ne rayayye da ya dace da kowane waje da zamani, kuma malamansa ba sa cakuda al’ada da ainihin musulunci, suna da dokoki da a kansu ne suke fitar da hukunci, hada da cewa kofar ijtihadi a wannan mazhabin a bude take har sai imam Mahadi (A.S) ya bayyana. Musulunci ba sandararren tunani ba ne, ya yarda mace ta yi ado, ta sa mai kyau, ta yi tunani, da jagorancin wasu abubuwa da suka dace da masalahar rayuwar dan Adam, kuma ta ci duk abin da take so kamar namiji, ta yi aure idan mijinta ya rasu.
|