Zabar Mace Ko Namijin Aure2- Nau’in sadakin da ake ayyanawa, ko kuma in ce kayan mun gani muna so da lefe a al’adunmu da ake sanyawa a kan saurayi, da idan suna da yawa yakan sanya jinkirin aurensa. 3- Kudaden kashewa domin bikin aure; 4- Tsanantawa wajen binciken laifuffukan juna; 5- Binciken matsayin dangin juna ta fuskacin wani mukami ko dukiya; 6- Makahon so da zai rufe idanuwan juna da zai sanya kowanne ya kasa ganin laifin dayan domin a lokacin suna kishirwar juna, amma da zaran sun kawar da wannan kishirwar sha’awar sai a gane laifin juna: Da man burinsa shi ne ya san ta a matsayin ‘ya mace, shi kenan sai ya yi wurgi da ita. 7- zargin juna da sukan yi ko son gaskiya ne ko na karya tsakanin duka bangarorin biyu na saurayi da budurwa, ta yadda dayansu yakan ji tsoron ko son gaskiya ko na karya dayan yake yi masa, ta yadda a nan gaba dayan su zai yi watse ya yi wurgi da abokin zamansa[6]. Rashin Aure Da Wuri Yakan Jawo Lalacewa
Saudayawa mukan ga samari da ‘yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin mutum idan ya balaga yakan zama kamar danyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe. Wannan al’amari na halitta saudayawa ya sanya wasu suka kasa kuma suka gajiya gaban sha’awarsu suka sallama mata, al’amarin da yakan janyo fasadi mai girma a cikin al’umma. Daga cikin irin wannan fasadi zamu yi kokarin kawo misali da daya ne daga ciki da ake cewa da shi istimna’i: Istimna’i wata mummunar dabi’a ce da takan samu samari ko ‘yan mata masu tashen balaga da sukan yi amfani da jikinsu ko hannunsu ko kayansu ko wani abu domin fitar da maniyyi daga garesu. Babbar musifar da istimna’i yake jawowa ta hada da: 1- Rauni da rashin karfin jiki; 2- Raunin kwakwalwa da kasa rike karatu ko kadan;
|