Zabar Mace Ko Namijin Aure



*Kada ki sa ran sai an yi miki abu irin na kawarki, ya kamata ki kula da iyakar mijinki da godewa, domin rashin hakan kan iya karya masa karfin yi miki hidima.

*Tsafta, magana mai sanyaya zuciya, da nisantar jayayya ko bakar magana, suna daga cikin sirrin zama mai albarka na soyayya da gina gida na gari da salihar al’umma.

*Kada a yi wa juna nasiha a gaban yara ko mutane, a bari sai hanakali ya kwanta an huta sannan sai a yi wa juna nasiha cikin wasa da dariya hakan yakan fi tasiri ga ma’aurata.

*A jawo kaunar juna da aiki ba da magani ba ko barazana.

*Kowa ya yi mu’amala da abokin zama da tausasawa ba da tsanantawa ba, domin ba ta magani sai dagula al’amuran zamantakewa.

*Kada mace ta sake ta bayar da fuska sai ga mijinta, haka ma kada ta sake ta tsananta wa mijinta, kuma ta sani kullum dole ta bujuro da kanta ga mijinta.

*Ba wa ’ya’ya isasshen lokaci da zama da su, da hira da su, da saita tunaninsu kan rayuwa.

*Girmama na gaba kamar uwar miji ko uwar mata yana daga kyawun zamantakewa da kargonta, wato girmama iyayen juna.

*Ba wa juna isasshen lokaci na tattaunawa da hira da warware matsalarsu.

*Tanadar kyauta ta musamman ga juna ta bazata ko kuma ga iyayen juna.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next