Zabar Mace Ko Namijin Aure



Musulunci ya zo da hana adon mace ga ajnabi da zai ja hankalinsa ko yaudararsa amma adon mace ga mijinta kowane iri ne, ko a cikin mata, ko wurin da babu ajnabi, ya halatta. Haka ma mace tana iya sa turare[41], amma idan zata fito waje sai ta sanya mai karancin kanshi da ba zai ja hankalin maza zuwa gareta ba, kuma tana iya yi wa mijinta ado da karin gashi[42], ko janfarce, da jan baki, ko zare, ko zane a fuska don kara kyau, ko sarka da zobe, da awarwaro don ado, da rina gashi da kowane launi domin ado, ko lalle[43], matukar ba ta yi ne don wani ba sai don mijinta kuma ba zata bayyana shi ga wasu mazaje ba[44]. Idan maras aure ce ya halatta ta kara gashi ta aikata sauran abubuwan da muka ambata amma da sharadin ba zata yaudari wanda yake son aurarta ba ya dauka nata ne na asali ba, wannnan kuwa an hana shi ne ta fuskacin yaudara[45].

Haka nan Musulunci yake kafa dokokinsa bisa masalaha da kuma kare hakkin iradar mutane matukar ba zai bude musu hanya ta fasadi ba wacce ta saba da hadafin halittar dan Adam. Abin takaici shi ne a duniyar musulmi an samu wasu masu nuna musulunci ga duniya da wata fuska daban. Saudayawa irin wannan al’amarin yakan jawo suka kansa har ya sanya makiyansa su rika yi masa wani kallo da ya sabawa hakikaninsa.

Rayuwa Da Juna A Cikin Gida

Mata idan mazajanku sun dawo daga wani waje yaya kuke tarbarsu: Shin kuna kula da yanayin yadda mai gida yake dawowa don kawar da damuwar da ya kwaso a waje? Ko kuna taya shi murnar farin cikin da ya shigo da shi na alheri da ya samo daga waje? Yaya rayuwarku da mazanku take a cikin gida?

 Wannan al’amari shi ne ya sa ake son aurar mace mai tausayi da hangen nesa da zabar wacce ta san ya kamata. Ku duba Uwar muminai khadija (A.S) har Manzo (S.A.W) ya yi wafati daidai da rana daya bai taba mantawa da ita ba, A tarihin Musulunci ya zo cewa ba abin da ya sanya Manzo (S.A.W) ya aure ta sai irin cikar hankali da tunani da ya gani, kuma ya same ta mace mai kyauta, da baiwa, da zurfin tunani. Duba ku gani daidai da rana daya ba ta ce masa ya bar abin da yake kai ba na kira zuwa ga Allah (S.W.T), Sai ma karfafarsa da ta rika yi, tana kuma gargadi ga masu kuntata masa, shi ya sa a rayuwarta da ita da Abu Talib (A.S) ba a taba samun wani ya samu da ma a kansa ba, amma bayan mutuwarsu sai ya zama tilas ne gareshi ya yi hijira har ma ya kira shekarar mutuwarsu da “Shekarar Bakin ciki”[46] Irin wadannan mata ba yadda za a yi a manta da ita har abada, Shi ya sa Manzo (S.A.W) ya zamanto yana son duk wani mai kaunarta, har ma ya kan yi umarni da a raba nama ga kawayanta[47].

Wani al’amarin shi ne binciken halin da mai gida ya samu kansa a waje wannan ba laifi ba ne, amma ba a son mace mai binciken mijinta da zargi ba tare da wani dalili ba, domin wannan yana iya jawo rashin fahimta tsakanin ma’aurata. Irin wannan ya faru ga wani bawan Allah da ya auri wata mata wacce al’adarsu ta bambanta ta wannan bangaren, ta kasance tana yawan tambayarsa da zargin ko ya je wajan wata ne, amma ka san bambancin al’ada yana da matsala ga aure idan ba a fahimci juna ba, domin ita a al’adunsu namiji kan yi wa mace bayanin duk inda ya je, alhalin shi yana ganin wannan takurawa ce da kuntatawa gareshi, mun kasance muna ba shi shawara da ya kula da cewa al’ada ce ta sa haka, a daya bangaren kuma akwai wadanda suke zuga shi kodayaushe da ya bar ta, har ma abin ya kai ga saki, amma bayan rabuwa shi da kansa ya gane cewa kuskure ne ya dawo mata, haka nan mace mai zargi ga miji take jawowa a sami matsaloli masu yawa har yakan iya kai wa ga saki.

Game da tattaunawa da mata a cikin gida da kuma taya su wadansu aikace aikace kuwa, akwai wadanda suka dauka cewa; ya zauna ya yi hira da matarsa? Ai sai ta rena shi! Abin mamaki shi ne: idan mata ba ta zama abokiyar hirar miji ba to waye abokin hirarsa? Da wanene yake son gina gidansa da al’umma ta gari? Sannan kuma don me bai ce zata rena shi ba yayin da yake neman auranta har yakan kai dare wajan zance?

Haka nan wani daga abokai ya gaya mini yana mai cewa: Matar abokin wansa ta aiko wa wansa shi yana wurin da cewa: Don Allah ya yi wa mijinsu nasiha ya rika yi musu hira da dariya, har ta kara da cewa; wallahi suna jin dadi idan suka jiyo dariyar mijin nasu da abokansa, don har lekowa suke su ga wai ko shi ne yake dariya! Kuma ta ce: Idan ta ga mace da mijinta ko a mota suna hira da dariya sai ta ji kamar a ce ma shi ne mijinta. Ku duba ku ga yadda sandararren tunani da jahiltar ma’anar rayuwa yake kaiwa!

Wasu malamai sun ce: Mace tana iya jure wa yunwa da wahala, amma ba ta iya jure wa nuna rashin so da kauna daga mijinta. Manzon rahama yana cewa: Zaman mutum a cikin iyalansa ya fi soyuwa wajan Allah (S.W.T) daga I’itikafi a masallacina wannan[48].

Amma sai ga shi ana cewa da mai zama a gida da iyalansa: Ai duk ya tare a gindinta sai abin da ta ce! Ballantana ma a ce yana kama mata wanke-wanke!; Ai shi ke nan an gama! Ai ta shanye shi! Ai magani ta yi masa! Wai an dauka rayuwa tare tana nufin bawa da uban gida ne, ko tana nufin a kuntata wa juna, ko kuma yanke alakar taimakekeniya ne!

Kuma bai isa ya zauna gida ba shi ma abin surutu ne, wato ko ranar hutu ce ko babu aiki sai ya fita ya shiga gari yawo don kar a ce ya tare a gida, amma wajan abokai a nan ya kwana dari ba komai, wani ma sai ya yi ta yawo bai san inda za shi ba kamar wanda ya tabu, da zaka tambaye shi sai ya ce yana dai yawo ne kawai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next