Zabar Mace Ko Namijin Aure



Wa Zaki/ka Zaba?

Lokacin da aka tashi neman abokin zaman tare yaya ya kamata a zabi juna? Menene ma’auni wajan zabar wanda za a aura? Wace fuska zamu futowa wanda zamu zaba? Shin yana daga cikin sharadi sai mai kudi ko mai shedar takardar digiri ko mai kaza da kaza?

Yayin zabar abokin rayuwar aure kada a yaudari juna kamar yadda samari suke yi, sai ya ari agogo, da takalmi, da mota, da karyar aiki, da karatau a jami’a, da tafiye tafiye, wannan bai halatta ba, domin kamar yadda aka hana mace canja kama da zata sanya ta yaudari masoyi haka ma namiji bai halatta ba ya yaudare ta, haramcin yaudara ya shafi duk bangare biyun, don haka mai son yin aure sai ya duba siffofi da shari’a ta kwadaitar da su kamar imani da takawa da salihanci.

Idan mace ba ta da siffofi na kamala takan canza gida ya zama kurkuku ne ga miji haka ma namiji, duba ka ga Annabi (S.A.W) da kansa yana addu’a yana cewa: “Ya Allah! Ina neman tsarinka daga matar da zata sa ni yin furfura tun kafin lokacin tsufana”[22].

Mu sani zabar abokin zama ba kamar zabar riga ko mota ba ne da za ta tsufa kayar ka sake wata, abin ba haka ba ne, don haka iyaye su sani wanene yake zuwa wajan ‘yarsu? Kuma wa za ta aura? Matukar mumini ne to su ba shi, sannan kada su dage a kan wanda ba ta so, ko sai mai kudi da makamantansu.

Hattara Da ‘Yan Zuga

Yawancin ‘yan mata sun iya yaudara da wasika, da murya mai dadi, da kwalliya, da sakin fuska, wasu ma da rangwada, amma da zaran an yi aure sai saurayi ya ga rana daya ta canja masa, sai ya shiga kokwanton komai game da ita yana ganin ta yaudare shi sai ya shiga jin haushinta ya daina kyautatawar da yake yi mata kafin aure, abokansa suna ce masa: Ango ka sha kanshi! yaya amarya? Shi kuma yana dariyar yake domin an riga an hura masa wuta a gidan.

Saudayawa wannan yana faruwa daga mummunar tarbiyya da ‘yan mata suke samu, imma daga mutanen gida ko daga al’adu marasa kyau, ko kuma daga ‘yan zuga da sukan ce da amarya: Ai kar ki yarda da namiji! Ai namiji ba dan goyo ba ne! Kar ki sake ki ba shi fuska, ya rena ki! musamman idan uwar zuga ta dace da maras wayo!.

Amma abin ba haka ba ne, sabanin haka ne dari bisa dari, domin idan kika kyautata wa namiji a lokacin ne zaki mallaki zuciyarsa, kuma ya kyautata miki, saudaywa wannan yana iya sanya shi mancewa da duk wata mace ba ke ba, kuma zaki ga ba ya tunanin wata sai ke, shi ya sa idan kika canza masa shi ma sai ya fara daure fuska, kamar yadda a bangaren maza ma a kan samu miyagun abokai masu bayar da bakar shawara.

Haka ma a kan samu mugwayen kawaye da sun rasa aure ko ba sa zama lafiya da na su mazan, don su kashe wa amaryar aure sai su zuge ta, irin wadannan abubuwa da ma wasu da ba mu ambata ba sukan sanya wasu amaren da zarar ango ya shigo sai su canza fuskar, don miyagun sun gama aiki, kafin ya shigo an kammala mata tsari kaf! Ba a bin da ya rage sai ta fada ramin da suka haka don gurbata rayuwa! Sai ka ga ana tambayar ango ya amarya? Sai ya rika yake yana dariya ta tilas, amma cikin gida tuni an mai da shi kamar Jahannama gareshi. Wani lokaci tayiwu ya kwaso zafi a waje wani ya bata masa rai, ya dawo gida sai ta caba masa, ta daba wuka a kan ciwon, wannan yakan iya sanyawa sai a yi aure wata daya, sai ka ga an rabu. Allah waddan masu kashe sunnar Annabi!

Jahiliyyar Da Aka Raya

Haka nan aka gurbata mana tarihin Musulunci aka ce: Ba a ba wa wanzami ko mai yin kaho aure ko mai saka, a yankunan hausa har da mai fawa dogaro da tatsuniyoyin da aka kirkiro na wai ya sayar wa Annabi (S.A.W) da naman kare maimakon akuya, wal’iyazu bil-Lahi! Har ma aka kirkiro cewa wanda ba bakuraishe ba ne ba tamka (tsara) ne na bakuraishiya ba, haka ma larabawa suna sama da waninsu, wannan duk Jahiliyyar da aka raya ce bayan Annabi (S.A.W).

Shi ya sa Imam Bakir (A.S) yayin da yake amsa wa Allaisi wanda ba ya daga cikin masu biyayya ga tafarkinsu da yake nuna ba zai aura wa mai saka ‘yarsa ba, sai ya gaya masa cewa: Me ya sa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa amma dai masaki ba tsara na ba ne. Sai imam Bakir (A.S) ya ce masa: Amma Allah ya yarda da aikinsa, ya kuma kaunace shi, ya kuma aura masa huurul’in, a yanzu kana kin wanda Allah yake kauna? Kana nisantar wanda yake tsaran ‘yan matan hurul’in don girman kai da shisshigi?. Don haka Musulunci ya sanya imani da musulunci su ne ma’auni da tamka ko tsara a aure babu wani abu bayan wannan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next