Hukunce - Hukuncedogara a kan ta kana ba sharadi ba ne a ce sai an sami yakini ko nitsuwa a kan haka, saannan kuma babu bukatar a wannan hali a ce za a binciko wata shaidar da ta saba hakan. AL-UDUL (CANZA TAKLIDI) T19: Shin ya halatta mutum ya bar taklidin A'alam cikin fararrun mas'alolin da suka shafi zamani saboda gazawarsa wajen ciro ingantattun hukuncinsu? A: Idan har shi mukallafi bai so ya yi ihtiyati cikin mas'alar ba, ko kuma ya gagare shi to idan har ya sami wani mujtahidi A'alam wanda yake da fatawa akan mas'alar to wajibi ne a gare shi ya koma gare shi ya yi masa taklidi. a cikin mas' alar. T20: Dangane da juyawa daga daya daga cikin fatawoyin imam khumaini (r.a), shin wajibi ne a koma ga fatawar mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da taklidin mamaci ? ko kuma ya halatta a koma ga fatawar sauran wasu mujtahidai? A: A nan wajibi ne a koma ga mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da takalidin mamaci. T21: Shin canza takalidi (al-udul) daga A'alam zuwa ga wanda ba A'alam ba ya halatta? A: Uduli a nan ya saba wa ihtiyat, hakika ma dai ba ya halatta a bisa ihtiyat idan har fatawar A'alam din akan mas'alar ta saba wa fatawar wanda ba A'alam ba. T22: Na kasance na ci gaba da taklidin. Imam (r.a)
|