Hukunce - Hukuncemujtahidin da ya cika sharudcfan taklid. T2: Nan ba da jimawa ba 'ya ta za ta cika shekarun balaga, inda daga nan wajibi ne gare ta ta zabi marja'in da za ta masa taklid, tattare da cewa gano hakan babbar matsala ce, don haka mene ne ya wajaba a gare mu? A: Idan har ita da kanta ba ta gano abin da ya wajaba a kanta dangane da wannan al'amari ba, to a nan abin da ya hau kanka dangane da ita shi ne tunatarwa da kuma shiryar da ita. T3: Wasu mutane wadanda ba sa da cikakkiyar masaniya yayin da muka tambaye su kan cewa ga wani maija'i suke yi wa "taklid", sukan amsa da cewa mu ba mu sani ba, ko kuma su ce muna wa wane (taklidi) ne. "sai dai kuma ba sa ganin cewa dole ne su koma ga risalarsa dan su yi aiki da ita, to anan mene ne hukuncin ayyukansu? A: Idan har ayyukan nasu sun yi daidai da "ihtiyat" ko kuma da abin da ya dace ko kuma ga fatawar mujtahidin da daman wajibi ne su koma gare shi, to ayyukan sun inganta ni T4: Wanda ya bar neman ilmin hukunce- hukuncen shari'a wanda suka dame shi shin ya aikata sabo ne ? A: Idan har rashin neman ilmin hukunce hukuncen zai kai shi ga barin aikata wa|ibai ko kuma ya kai shi ga aikata haramun, to ya aikata sabo. SHARUDDAN TAKLID T5: Shin ya halatta yin "taldik" ga mujtahidin da ba marja'i ba Kana bai da risala?
|