Hukunce - Hukuncemasa takalidi daga cikin Fukaha'u to ya ta'ailaka ne ga shi kansa mukallaf. T8: Shin A’alamiyya (fifikon marja'i bisa sauran' yan uwansa) sharadi ne cikin taklid ko kuma a'a ? kana yaya ake gane Aalamiyya? A: A bisa Ihtiyat wajibi ne yin taklid ga A'alam cikin mas'alolin da fatawoyinsa suka saba da fatawoyin sauran maraji'ai. Kana Aalamiyya shi ne ya kasance ya fi sauran mujtahidai kudura kan sanin hukunce hukuncen ubangiji da kuma kuduran ciro hukunce hukuncen daga inda ake ciro su. kana kuma masaniya kan zamaminsa-gwargwadon abubuwan da suka shafi hukunce- hukuncen sharia da kuma sanin zamani ta yadda zai bayar da ra'ayin fikhu gwargwadon yadda ya dace da shari'a- shi ma yana daga cikin ababen da ke yin tasiri a ijtihadi. T9: Shin za'a iya hukunta, taklidin wanda ya yi takalidi ga wanda ba A'alam ba saboda zaton cewa shi A'alam da bai mallaki sharuddan taldid ba, shin za a hukunta irin wannan taklidi da cewa bai inganta ba ? A: Ba ya halatta bisa ihtiyat yin taklidi ga wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da aka samu sabani a cikinsu saboda kawai zaton rash in mallakan sharuddan A'alamiyya ga A'alam. T10: Yayin da aka bayyana wasu malamai da cewa su ne A'alam a cikin wasu mas'aloli (ta yadda ko wani daya daga cikinsu A'alam ne a cikin wasu takamammun mas'aloli). Shin ya halatta komawa gare su ko kuma a'a? A: Rarraba taklid babu matsala a cikinsa, ballantana idan har A'a lamiyyar kowane daya daga cikinsu ta zamana akan mas'alar da yake masa takilidi ne to a wannan hali wajibi ne bisa ihtiyat ya rarraba taklid idan har fatawdyinsu sun bambanta. T1l: Shin ya halatta taklidin wanda ba A'alam ba tare da cewa akwai a'alam?
|