Hukunce - HukunceT45: Kamar yadda ci gaba da takalidin mamaci ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi bisa yadda fatawar malamai ya tafi akai, to shin umarni da hukunce -hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen jagoran da ya rasu su ma suna bukatan izinin sabon (rayayyen) jagora kafin su ci gaba da wanzuwa ko kuma a'a? A: Hukunce- hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen "waliyi amril muslimin" da ya rasu in dai har ba na takaitaccen lokaci ba ne, to tana nan daram, sai dai idan sabon jagoran yana ganin akwai wata maslaha wajen shafe su, to yana da daman shafe su. T46: Shin wajibi ne ga fakihin da yake zaune a jamhuriyar musulunci ta A: Wajibi ne ga kowane mukallaf, ko da kuwa mujtahidi ne, da ya yi biyayya ga hukunce-hukuncen jagoranci(hukuma) na waliy amril muslimin, ba ya halatta ga wani ya saba wa jagoran da yake jagoranci saboda da'awar cewa shi ya fi shi dacewa, hakan kuwa wajibi ne idan har shi jagoran da yake jagorancin ya hau wannan matsayin ne ta hanya da ta dace da dokokin da aka tsara domin haka, to amma in ba ta wannan yanayin ba, to al’amarin ya bambanta. T47: Shin mujtahidin da ya cika sharudda a zamanin Buya (gaiba) yana da ikon zartar da haddi? A: Wajibi ne a gudanar da haddi a lokacin gaiba, ikon hakan kuwa yana hannun waliyi amril muslimin ne kawai. Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria
|