Bidi’a A Cikin Addini



Sannan Kur’ani yana Allah-wadai da yahudawa da nasara yayin da suka rubuta wasu abubuwa da hannayensu sannan suka jingina shi zuwa ga Allah don isa zuwa ga wasu gurikan na abin duniya. Ga abin da yake cewa a kan hakan: “Banu ya tabbata ga wadanda suke rubuta littafi da hannayensu sannan su ce wannan daga Allah yake, domin su sayar da shi da kudaden ‘yan kadan, to banu ya tabbata a garesu a kan abin da suka rubuta da hannayensu, sannan banu ya tabbata garesu dangane da abin da suke kasuwanci da shi”. [15]

Mun ga Matsayin Kur’ani dangane da wadanda suke bidi’a a cikin addini da kuma wadanda suke canza wani abu daga cikin addini a matsayin masu yin wasa da hukuncin Ubangiji. Sannan dole ne a nan mu fadakar a kan cewa matsayin ruwayoyi kuwa a bidi’a kamar matsayin Kur’ani ne a kan hakan: Manzo da Shugabannin musulunci sun kasance suna tir da bidi’a da masu yin bidi’a wato masu yin wani abu a cikin wanda ba shi da tushe daga addinin, suna ambatarsu da masu bidi’a kuma batattu. Yana da kyau a nan mu tunatar a kan wani hadisi wanda malaman addinin musulunci suka ruwaito daga Manzo, sannan sukan yawan karanta shi a cikin hadubar sallar jumu’ar manzo a cikin daya daga cikin hudubobinsa yana cewa:

“Fiyayyen abu shi ne littafin Allah, sannan fiyayyar shiriya ita ce shiriyar Muhammad (s.a.w), Sannan mafi sharrin abu shi ne abin da a ka kirkira, Sannan duk abin da yake bidi’a bata ne”.

Bugu da kari ma a kan haka, hankali ma yana Allah-wadai da yin bidi’a a cikin addini, domin kuwa yin hakan ketara iyaka ne zuwa ga hakkin da ya kebanta ga Allah kawai madaukaki. Sannan kuma tare da yin karya da kirkira wa Allah abin da ba daga gare shi yake ba, saboda haka muni da haramcin yin hakan a fili yake ba shi da bukatar bayani da yawa a kan kan hakan.

Bayanin Bahsin Da Ya Gabata A Takaice

1-Muna iya samun sakamako dangane da bahsimmu da ya gabata kamar haka:

Kafa doka hakki ne na musamman wanda ya kebanci Allah shi kadai, saboda haka duk wani nau’i ne na shigar shugula ga hakkin da ya kebanci Allah. Saboda haka wani abu ne wanda yake mummuna a mahangar hankali da shari’a kuma wani abu ne wanda aka yi hani a kansa kuma haramun.

2-Kebantuwar Kafa doka ga Allah kuwa ya kasance ne sakamakon cewa kafa doka yana bukatuwa zuwa ga wasu abubuwa kamar haka:

1-Cikakkiyar masaniya dangane da mutum.

2-Rashin duk wani amfani ga kafa dokar dangane da wanda yake kafa dokar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next