Bidi’a A Cikin AddiniA nan sakamakon ka’idojin na hankali mun ga yadda kafa doka ta takaita kwai ga Allah madaukaki. Abin da ya rage a nan shi ne mu ga me Kur’ani yake cewa dangane da haka: Dangane da wannan magana kuwa Kur’ani shi ma ya karfafa hukuncin da hankali ya yi ne domin kuwa shi ma ya tabbatar da cewa babu wani wanda yake da hakkin kafa doka sai Allah madaukaki. Ayoyi da dama ne kuwa suka bayyanar da wannan magana, a nan dmin mu takaita kawai zamu kawo wasu ne daga cikin wadanda suke yin magana a kan hakan: 1-â€Babu hukunci sai ga Allah, kuma ya yi umrni da cewa kada a bauta kowa sai shi kuma wannan shi ne addini tsayayyeâ€.[3] Jumlar da take cewa “babu hukunci sai ga Allahâ€tana bayyanar da cewa duk wani nau;in hukunci ya kebanta da Allah ne kawai. Sakamakon cewa shi kadai ne yake da wannan ikon don haka ya ce shi kawai za a bauta wa. 2-Ahlul kitab Sun dauki malamansu da Annabi Isa a matsayin ubangijinsu, sabanin Allah madaukaki[4]. Wannan aya tana bayyanar da yadda Ahlul kitab suka dauki hakkin da Allah ne kawai yake da shi suka mika wa malamansu, mai makon su koma zuwa ga Littattafan da aka aiko musu wajen samun hukunce-hukunce, sai su koma zuwa ga malamansu batattu, duk da kuwa sun san cewa wani lokaci sakamakon wasu dalilai suka halatta abin da Allah ya haramta su kuma haramta abin da Allah ya halatta, sakamakon haka ne ta bangaren kadaita Allah a wajen kafa doka suka kasance mushrikai. Addi Bn Hatim ya kasance kirista yana cewa: Yayin da shigo wajen mazon Allah a lokacin yana karanta wannan ayar wacce ma’anar ita ce “Kiristoci da yahudawa sun kasance sun dauki malamansu a matsayin ubangijinsuâ€. Sai na cewa Manzo wannan al’amari ba shi da inganci. Sai Manzo ya ce: Sukan halatta haram su kuma haramta halas, sannan kuma kuna yi musu biyayya ko ba haka ba ne? Sai na ce haka ne. Sai ya ce: to wannan kawai ya wadatar ya zamana kun dauke su matsayin ubangijinku[5]. Tare da la’akari da abin da muka fada a sama a cikin wannan Bahasi zamu fahimta cewa kafa doka kawai ya takaita ne ga Allah mai tsarki. Sannan ayyukan annabawa da imamai ne suke kawai bayyanar da wadannan doki na Allah madaukaki, sannan ba su da ikon sanya hannu a cikin kafa dokokin Ubangiji. A nan amsar wata tambaya guda daya kawai ya rage wannan kuwa ita ce, idan hakkin kafa doka kawai ya takaita ga Allah ne, to a jamhuriyar musulunci menene matsayin kafa dokar da ‘yan majalisa suke yi? Amsar wannan tambaya kuwa ita ce, aikin ‘yan majalisa shi ne shirya ayyuka a karkashin dokokin na baki daya da musulunci ya zo da su, don haka ba suna kafa dokoki sababbi ba ne. Sannan babu wata kasa duk yadda ta kai wajen ci gaba wajen dokoki ta zamana ta wadatu da shirya abin da ya kamata ta yi (programs) Saboda haka a hakikanin gaskiya Majalisa wani wuri ne na shirye-shiryen abin da ya kamata gwammanati ta aiwatar karkashin dokokin addinim musulunci. Sannan ta nuna yadda ya kamata a aiwatar da wadannan dokokin acikinrayuwar dan Adam ta yau da kullum.
|