Bidi’a A Cikin Addini



Da yawa daga cikin mutane tare da amfani da wasu ra’ayoyi nakansu suna ganin bidi’a a cikin addini wani nau'i ne na girmamawa, misali hukuncin musulunci ya nuna cewa haramun ne yin azumi ga matafiyi. Lokacin da Manzo ya yi tafiya domin bude garin Makka ya kasance a cikin watan Ramadan ne, sakamakon haka lokacin da ya isa wani wuri sai ya yi umarni da a kawo masa ruwa ya sha. Amma wasu daga cikin musulmi da tunanin girmama abu ba tare da wani tunani ba sai suka saba wa Manzo a kan hakan sai ba su sha azuminsu ba. Domin kuwa sun yi tunanin cewa idan suka yi yaki tare da azumi zai fi lada. lokacin wannan labari ya je ga kunnen Manzo Sai ya kira su da masu sabo kuma masu zunubi. [16]

2-Bin zabin abin da mutum yake sha’awa

Kowane abu a cikin musulunci yana da hukunci guda daya ne. Mafi yawa daga cikin sabanin da ke akwai tsakanin musulmi dangane da hukunce-hukunce ya samu asali ne daga bin son zuciya. Da wani kalamin domin girmamawa muna iya cewa ya samu tushe ne daga bin abin da mutum yake sha’awa. Imam Ali (a.s) a cikin maganganunsa yana nuni da wannan al’amari kamar haka: “Yaku mutane kodayaushe fitinu suna faruwa ne daga bin son zuciya ta yadda mutum zai bi abin da yake so sabanin abin da Kur’ani ya zo da shi”. [17]

Ana iya samun sheda da yawa a cikin tarihi a kan ire-iren wannan bidi’a, saboda haka a nan muna iya wadatuwa da misalai guda biyu daga cikinsu:

A: Daya daga cikin kashe-kashen hajji ita ce hajjin “tamattu”. Wannan wani nauyi ne da ya hau kan kowane musulmin da yake rayuwa mil 48 daga Makka ko fiye da haka, saboda haka wanda hajjin tamattu ya hau kansa, dole ne bayan ya gabatar da umura sai ya fita daga cikin harami, sannan a wannan lokaci duk wani abu wanda ya haramta gareshi banda farauta ya halatta gareshi, har zuwa ranar 9 ga Zulhajji inda zai sake yin harami domin gabatar da sauran ayyukan hajji.

Tarihi yana rubuta cewa a zamanin Manzo wani daga cikin sahabban Manzo bai yi na’am ba da wannan hajji ta tamattu domin kuwa bai yi masa dadi ba a kan cewa yaya za a yi mutum ya zo aikin hajji tsakanin umura da hajji ya iya saduwa da iyalinsa ko kuma a lokacin da ruwan wanka (janaba) yake sakkowa daga fuskarsa kuma ya yi haramin aikin hajji, ta haka ne lokacin da ya zama halifa sai ya hana musulmi wannan hajji ta tamattu, alhalin wannan ya sabawa umurnin Allah da manzonsa. Saboda haka yana daya daga cikin bidi’a a cikin addini, wanda yake ba wani abu ne sai binson zuciya da abin da mutum yake ganin shi ne ya fi a kan kansa. Amma abin farin cikin wannan hani da halifa na biyu ya yi ya kasance na wani lokaci ne, inda yanzu da yawa daga cikin musulmi ‘yan Sunna kamar yanda ‘yan Shi’a suke yin hajji tamattu suma suna wannan nau’i na hajji.

B: Malik shugaban mazhabar Malikiyya yana ruwaitowa cewa: mai kiran salla ya zo wajen Umar Bn Khattab domin ya sanar da shi cewa lokacin salla ya yi, sai ya samu khalifa yana barci, domin ya tayar da khalifa daga barci sai ya ce: “Assalatu khairum minan naum”. Wato salla tafi barci. Sai khalifa ya ji dadin wannan jumla sai ya karanta a cikin kiran sallar asubahi”.[18]

3-Ta’assubanci marar dalili

Daya daga cikin abubuwan da suka kawo bidi’a a cikin addini shi ne, ta’assubanci (riko da abu) marar dalili a kan al’adun iyaye da kakanni, da kuma al’adun da mutum ya tashi a cikinsu. Tsananin soyuwar da mutum yake da shi dangane da wadannan abubuwan yakan sanya shi ya yi nesa da fahimtar gaskiyar addini ta yadda zai mai da bata a mai makons gaskiya.

Tarihi yana nuna cewa: Mutanen Da’ifa sun aiko mutane zuwa ga Manzo domin su wakilce su domin su su bayyana wa Manzo shirinsu domin karbar addinin musulunci, amma sai suka sanya wa musulunci sharudda guda kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next