Bidi’a A Cikin Addini1-Ya zamana ya halasta musu riba. 2-Ya halasta musu kusantar matan banza. 3-Wuraren bautar gumakansu su kasance har zuwa shekaru uku masu zuwa. Lokacin da Manzo ya samu labarin wadannan sharudda nasu sai ya nuna tsananin damuwarsa kuma ya nuna rashin amincewar da ko daya daga cikinsu. [19] Idan da mutanen Da’ifa sun kasance musulmii na hakika, to dole ne su mika wuyansu ga hukuncin Ubangiji, ba wai su gabatar da son zuciyarsu ba a kan musulunci. Wannan a fili yake sakamakon manufofinsu daban-daban ya sanya suka sanya wa addinin wadannan sharudda. Daga cikin neman da suka yi kuwa na ci gaba da bautar gumaka, wannan kuwa duk ya faru ne sakamakon ta’assubanci marar dalili. Wadannan dalilai guda uku na sama da wadansu makamantansu su ne tushen bidi’o’i a cikin addini. Sannan akwai wasu dalilai ma bayan wadannan amma saboda karancin damar da muke da ita zamu takaita a nan. Fito Na Fiton Addini A Kan Hana Bayyanar Bidi’a Malamai da masana da addinin musulunci kowane lokaci sun kasance suna kokari a kan hana shigowar bidi’a a cikin addini, sannan wannan ya wajaba a kansu domin kula da abin da wasu wadanda wasu daga cikin masu magana da yawon addini da marubuta, ta yadda zasu kula da abin da suke fada domin sukan yi amfani da kalmomi masu jan hankali domin su shigo da sabbin abubuwa a cikin addini. Sannan wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi kariya a kan addini duk inda yake, ta yadda addini zai kasance kamar yadda ya zo daga Allah madaukaki ba tare da wani canji ba. Kamar yadda ya zo daga Manzo kuma dukkan Sunna da Shi’a sun tafi a kan hakan cewa: Manzo ya ce wa al’umma da su koma zuwa ga Kur’ani da koyarwar Ahlul baiti (a.s) idan suka yi riko da wadannan abubuwa guda biyu, ba zasu taba bata ba daga hanyar daidai, inda yake cewa: “Na bar muku nauyi guda biyu littafin Allah da Ahlul baiti wadanda idan kuka yi riko da su ba zaku halaka ba har sai kun koma zuwa wurina a bakin tafkiâ€.[20] Sannan a wani hadisin an siffanta iyalan Manzo ne da jirgin annabi nuhu da cewa duk wanda ya shige shi ya tsira wanda kuwa bai shiga ba ya halaka domin zai nutseâ€.[21] Duk lokacin da al’ummar musulmi suka karbi addininsu daga iyalan Manzo tabbas zasu samu cikakkiyar shiriyar Ubangiji, sannan zasu tsira daga duk wata bidi’a da bin masu bidi’a.
|