Bidi’a A Cikin Addini3-Ya zamana ya yadu cikin al’umma: Daya daga cikin sharuddan kasancewar sabon abu ya zama bidi’a shi ne, ya zama ya yadu a cikin mutane. Duk da cewa wannan sharadi bai zo a wajen bayyana ma’anar ‘bidi’a’ ba amma hakikanin ‘bidi’a’ yana kunshe da shi. Sannan akwai abubuwa da yawa da suke nuni a kan hakan. Misali ya zo a cikin ruwayoyin inda suke nuni a kan fito na fito da ‘bidi’a’ masu yin bidi’a babu shakka wadannan ruwayoyin sakamakon yaduwar wannan bidi’o’i ne a tsakanin al’umma ta hanyar masu yin wannan aiki. Manzo mai tsira yana cewa: “Duk wanda ya zo da bidi’a a cikin wannan addinin zunubbin wadanda suka bi shi a kan hakan yana a kansaâ€[12]. Wannan ruwaya da makamanciyarta suna nuni ne a kan cewa tunanin kari ko ragi a cikin addini matukar bai wuce matsayin tunani ba wato bai kai ga aiki ba ta yadda kawai ya tsaya ne ga mai shi, wato bai yadu zuwa ga sauran mutane ba, to a nan haramun ne kawai amma ba bidi’a ba ce. Tare da kula da wadannan sharudda da muka ambata na bidi’a muna iya fahimtar hakikanin ma’anar bidi’a sannan mu fahimci iyakokinta ta yadda zamu iya gane abin da ba ita ba. Haramcin Bidi’a A Cikin Kur’ani Da Sunna Bidi’a wani nau’i ne na shiga a cikin hakkin tafiyar da al’amura (rububiyya) domin kuwa al’amarin kafa doka ya kebanci Allah ne kawai, saboda haka duk wani nau’i na shiga a cikin tafiyar da al’amura yana da hukunci shiga cikin hakkin Allah madaukaki. Sannan jingina abin da ba shi da asali daga addinin zuwa ga Allah ko manzanninsa, yana daga cikin kirkira wa Allah da manzanninsa wani abu wanda ba daga garesu yake ba (Iftira). Sakamakon haka ne Kur’ani yake Allah wadai da bidi’a. Misali dangane da mushrikai inda suka raba ranakun Allah ba tare da wani dalili ba, ta yadda suka sanya wasu ranaku halas wasu kuwa haram, sannan suka jingina wannan aiki nasu zuwa ga Allah, a kan haka ne Kur’ani yake cewa: “Shin Allah ne ya yi muku izini a hakan ko kuwa kuna kirkirawa ne ku dangana shi zuwa ga Allah?â€[13]. Sannan yana cewa: “Kada ku ce wannan halas ne wannan haram ne daga abin da kuke fada na karya daga bakunanku, domin ku kirkirawa Allah karya, tabbas wadanda suke kirkirawa Allah karya ba zasu rabauta baâ€[14]. Zargin da Allah yake wa masu bidi’a a cikin wannan ya kasance ne sakamakon yadda suka shiga cikin hakkin Allah na kafa doka sannan suka dangana shi zuwa ga Allah. Wato ta yadda suke halastawa ko suke haramtawa ba tare da izinin Allah ba, kuma su jingina abin zuwa ga Allah.
|