Halayen Imam Bakir (a.s)



2. Kisan da Umayyawa suka yi wa Imam Husain (a.s) a Karbala.

3. Halartawar da Umayyawa suka yi wa Madina a waki'ar Hurrat.

4. Jifan da Umayyawa suka yi wa Ka'aba da majaujawa.

5. Bore da yunkurin Alawiyyawa daya bayan daya da nufin kifar da gwamnatin Umayyawa.

6. Bin son zuciyar da mafi yawancin shugabannin Umayyawa suka yi. Da sabawarsu ga shari'ar Musulunci a cikin dabi'unsu.

7. Rashin ko in kula ta Umayyawa a game da matakin musulmi na rashin amincewa da su. Da kuma dagewar Umayyawa a kan ayyukansu munana.

Imam Al-Bakir (a.s) ya rasu a Madina a shekara ta 114 bayan hijira, sakamakon guba da aka ba shi ta hannun Hisham dan Abdulmalik.

Daga Cikin Shiryarwarsa: 1. Ya kai dana! Ka guji kasala da kunci domin su mabudi ne na dukkan sharri, idan ka yi kasala ba zaka iya sauke wani hakki ba, kuma idan ka kosa ba zaka iya yin hakuri a kan wani hakki ba.

2. Ya ishi mutum aibu ya yi hakuri da mutane a kan abin da yake shige masa duhu ga kansa, ko ya umarci mutane da abin da ba zai iya barin sa ba, ko kuma ya matsanta wa abokin zamansa da abin da bai shafe shi ba.

3. Hakika wannan harshen mabudin dukkan alheri da sharri ne. Don haka ya kamata mumini ya kame harshensa (ya rufe bakinsa) kamar yadda yake boye Zinariyarsa da Azurfarsa. Domin manzon Allah (s.a.w) ya ce: Allah ya ji kan muminin da ya kame harshensa daga dukkan sharri.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next