Halayen Imam Bakir (a.s)Sai wannan kirista ya musulunta! Ya kasance kogi ne a ilimi kamar kumfa mai tunkuda, yana amsa kowace tambaya aka tambaye shi ba tareda tsayawa ba. Ibn Ada Makki yana cewa: ban taba ganin malamai sun kaskanta a gaban wani mutum ba kamar yadda suke a gaban Bakir (A.S), na ga Hakam bn Utaiba -duk da girmansa- a gabansa kamar wani yaro gaban malaminsa. Muhammad dan Muslim yana cewa: Babu wani abu da ya taba zuwa zuciyata sai da na tambayi Muhammad dan Ali (A.S) har sai da na tambaye shi tambayoyi dubu talatin. Ya kasance mai yawan ambaton Allah har sai da dansa Imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: Babana ya kasance mai yawa zikiri, ina tafiya tare da shi amma yana ambaton Allah, kuma ya kasance yana magana da mutane amma wannan ba ya shagaltar da shi daga ambaton Allah[5]. Ya kasance mai yawan tahajjudi da ibada mai yawan kuka da zubar hawaye. Imam Al-Bakir (a.s) ya karbi Imamanci bayan rasuwar mahaifinsa Imam Ali dan Husain (a.s) a shekara ta (94 bayan hijira). Daga cikin muhimman ayyukan da ya yi su ne: 1. Farfado da harkar Ilimi na Musulunci bayan girgizar da ta yi tun a lokacin mulkin Mu'awiya dan Abu sufyan. 2. Tayar da harkar Shari'ar Musulunci –a kebance– wacce ta dawo wa fikihun Musulunci matsayinsa a cikin rayuwar Musulunci. Lokacin da Imam Al-Bakir (a.s) ya rayu ya yi dai dai da karshen mulkin Umayyawa, da yin raunin hukumar Umayyawa a kaskantuwar sakamakon faruwar abubuwan da suka taimaka wajen raunin daular da faduwarta, duk sun taimaka wa Imam Muhammad Bakir (a.s) wajen aikata wadannan ayyukan. Muhimman wadannan abubuwa wadanda suka taimaka wajen faduwar daular Umayyawa su ne: 1. Kisan da Umayyawa suka yi wa jagororin tunani da kawo gyara daga cikin musulmai, kamar: Maisam attammar, da Rashid al-hijri, da Amru bn Hamk al-khuza'i, da Hijr bn Udayyil kindi.
|