Halayen Imam Bakir (a.s)Imam Al-Bakir (a.s) ya karbi Imamanci bayan rasuwar mahaifinsa Imam Ali dan Husain (a.s) a shekara ta (94 bayan hijira). Daga cikin muhimman ayyukan da ya yi su ne: 1. Farfado da harkar Ilimin musulunci bayan girgizar da ta yi tun a lokacin mulkin Mu'awiya dan Abu sufyan. 2. Tayar da harkar Shari'ar musulunci wacce ta dawo wa fikihun musulunci matsayinsa a cikin rayuwar musulunci. Lokacin da Imam Al-Bakir (a.s) ya rayu ya yi dai dai da karshen mulkin Umayyawa, da yin raunin hukumar Umayyawa a kaskantuwar sakamakon faruwar abubuwan da suka taimaka wajen raunin daular da faduwarta, duk sun taimaka wa Imam Muhammad Bakir (a.s) wajen aikata wadannan ayyukan. Muhimman wadannan abubuwa wadanda suka taimaka wajen faduwar daular Umayyawa su ne: 1. Kisan da Umayyawa suka yi wa jagororin tunani da kawo gyara daga cikin musulmai, kamar: Maisam attammar, da Rashid al-hijri, da Amru bn Hamk al-khuza'i, da Hijr bn Udayyil kindi. 2. Kisan da Umayyawa suka yi wa Imam Husain (a.s) a Karbala. 3. Halartawar da Umayyawa suka yi wa Madina a waki'ar Hurrat. 4. Jifan da Umayyawa suka yi wa Ka'aba da majaujawa.
|