Halayen Imam Bakir (a.s)



Matakin ganin bayansa ta hanyar kaga masa wasu laifuffuka domin a rusa ismarsa, mun ga wannan kagen ya maimaitu a zamunan baya a hannun Ibn taimiyya da Zahabi na nuna fifikon wasu mutane kamar Abizzinad, da Katada, da Rabi'a a kansa.

Matakin ganin an kakaba masa cewa ya yabi halifofin farko, har sai da aka jingina masa cewa; su 'ya'yan manzon Allah (s.a.w) sun yi ittifaki a kan yabon halifofin farko, hatta da Darkudni ya ruwaito wasu maganganu da suke masu rauni kuma na kage a kan irin wannan, al'amarin da aka yi nuni da yardar imam Bakir kan abin da ya gudana, wanda yake lizimtar inkarin cancantar Ali (a.s). (Assawa'ikul Muhrika: Ibn Hajar: 78).

Matakin ganin sun nuna rauninsa, da yabon ra'ayin Abuhanifa a wata tattaunawa tare da shugaban masu ra'ayi da kiyasi a cikin fikihun musulunci Abuhanifa. Sai aka nuna yadda imam Bakir ya rungumi Abuhanifa bayan ya kafa masa hujja da cewa; namiji ya kamata ya samu kaso daya mace kuma kaso biyu domin ta fi shi rauni!. Aka nuna Abuhanifa da ya durkusa gaban imam Bakir amma sai imam Bakir ya kamo hannunsa ya tayar da shi ya rungume shi!. (Imam Sadik: AbuZuhra; s 22-23.)

Sun manta cewa; babu wani abu da ya gama tattaunawar Abuhanifa da imam Bakir (a.s), domin Abuhanifa ya zo Madina ne lokacin imam Sadik, kuma nasihar da imam Sadik (a.s) ya yi masa ta zo a littattafai masu yawa. Wannan shi ne abin da ya zo kamar haka:

Imam Sadik (a.s) ya ce masa:  Ka ji tsoron Allah kada ka yi kiyasi a addini, ka sani farkon wanda ya yi kiyasi shi ne Iblis. Har dai ya tambayi Abuhanifa cewa: Me ya fi muni: kashe rai ko zina? Sai Abuhanifa ya ce: Kashe rai. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Allah ya karbi shedu biyu a kisa, amma bai karba ba a zina sai guda hudu. Sannan ya sake ce masa: Me ya fi girma; salla ko azumi? Sai Abuhanifa ya ce: Salla. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: To yaya mai haila take rama azumi amma ba ta rama salla? Yaya to da hakan zaka rika yin kiyasi a addini! Ka ji tsoron Allah ka bar kiyasi. (alwasa'il: abwabu sifatil kadhi: babi 6, j 18, s; 29)

Idan mutum ya duba irin wannan lamarin sosai zai ga yadda alayen manzon Allah (s.a.w) suka sha wahala matuka sosai domin su kare shari'ar Allah.

Rashin yin wani motsi na siyasa da yakar daula daga wurinsu, da shagaltuwa da ilmantar da duniya hakikanin sakon Allah bai hana miyagun sarakuna neman ganin bayansu ba. Don haka ne muka ga Hisham duk da saninsa da cewa imam Bakir ya shagaltu da ilmantar da mutane ne amma bai kyale shi daga karshe sai da ya sanya wanda ya yi masa makirci aka shayar da shi guba da ta yi sanadiyyar rayuwarsa.

Domin gudun tsawaitawa a nan zan dakata, sai dai zan kawo rayuwar imam Muhammad Bakir (a.s) a takaice kamar haka:

Shi ne: Muhammad dan Ali dan Husain dan Aliyyu bn Abi Dalib (a.s).

An haifi Imam Muhammad al-bakir (a.s) a Madina a shekara ta (57 bayan hijira).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next