Halayen Imam Sajjad (a.s)Ya kasance daga tsananin tsantsenninsa yana salla a wuni da dare raka'a dubu, idan lokacin salla ya yi sai fatar jikinsa ta tashi kuma ya yi yalo ya rika makyarkyata, kuma daga lakabobinsa akwai mai saba saboda kufai na sujada a goshinsa da tafinsa da gwiwarsa. Wani mutum ya zage shi wata rana ya gaya masa bakar magana shi kuma (a.s) yana shiru bai yi magana ba, bayan wani lokaci sai ya zo wajen sa, sai mutanen da suke nan suka yi tsammanin ya zo ne ya rama, sai ya karatanta ayar nan: "Da masu hadiye fushi kuma masu rangwame ga mutane kuma Allah yana son masu kyauttawa"[3]. Sannan sai ya tsaya kan wannan mutumin ya ce: ya dan'uwana ka tsaya a kaina da zu ka ce kaza da kaza, idan abin da ka fada akaina haka ne to ina neman gafarar Allah, amma idan abin da ka fada ba haka ba ne to Allah ya gafarta maka[4]. Imamancinsa: Imam Ali dan Husain (a.s) ya karbi Imamanci bayan shahadar mahaifinsa Imam Husain (a.s) a shekara ta (61 bayan hijira). A cikin tsawon lokacin Imamancinsa ya ga rashin Imani da kekashewar zuciya mai tsanani daga matsantawar da gwamnatin Umayyawa ta yi masa. Sun saka masa tsaro mai takurawa, kuma sun ajiye masa masu leken asiri, domin kada ya ci gaba da harkar da’awar Musulunci wacce mahaifinsa Imam Husain (a.s) ya ciyar da ita gaba ta hanyar sadaukar da ransa da ya yi a ranar Karbala. Sai dai cewa gaba dayan abubuwan da suka aiwatar, da riga kafin Umayyawa a game da Imam Ali dan Husain (a.s) bai iya hana shi ci gaba da harkar da’awar musuluncin ba. Ya riga ya dauki wasiyyoyi da kira, a matsayin wata hanya ta yada Musulunci da yakar Umayyawa. An tattara da yawa daga cikin addu’o'insa a cikin littafi guda daya aka kira shi da suna "Assahifa Assajjadiyya". Assahifa Assajjadiyya: Wani tari ne daga addu’o'in Imam Ali dan Husain (a.s). An tattara Assahifa kuma an wallafa ta a zamanin Imam Ali dan Husain (a.s), kuma an rubuta ta guda biyu. Imam Muhammad al-bakir ne ya ajiye guda daya Imamai ma’asumai suka gaje ta a bayansa, daya Kuwa: wacce Zaidu (R) ya ajiye ta a gurinsa, â€کya’yansa suka gaje ta a bayansa.
Sannan daga baya malamai sun wallafa wasu littattafan wadanda suka kunshi addu’o'in da suke cikin wadancan littattafan guda biyu na farko tare da dan kari kadan ko ragi. Assahifa tana da babban muhimmanci a gurin musulmai, sun kula da ita babbar kulawa, kuma ba zata gushe ba tana abar kulawa da ba wa muhimmanci. Muhimmancinta yana bayyana a cikin abubuwa masu zuwa:
|