Halayen Imam Sajjad (a.s) Salon tattaunawa da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni, kamar yadda ya zo a Addu’ar Kumail Bn Ziyad: “Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, kuma suna yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba.â€‌ Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa, da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada, kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sannan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa ta wani bangare a boye, domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa idan har bai aikata shi ba. Karanta wani salon addu’ar da a ke neman uzuri a cikin ta da cewa: “Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!â€‌. Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (s.w.t) ne, da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa, don soyayya da bege gare shi, da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya fi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta, to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu’ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah, yadda zai yafe, kuma ya yi masa rangwame. Mamakin taushin wannan salo na kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubai, ba zai buya ba. Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu’a da ta kunshi kyawawan dabi’u, da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowane mutum ya siffantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo: “Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da’a, da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai, da daidaita harsunanmu, da daidaito, da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha’inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa’aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al’umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta musu na daga hajji da umra don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahamaâ€‌. Kuma ni ina mai wasiyya ga â€کyan’uwana masu karatu da cewa, kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi, tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (a.s), Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai, kuma ba ta kara wa mutum sani, ba ta sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki, kuma ba a amsa masa addu’a da haka. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka, sannan ka ji cewa lalle za a amsaâ€‌[1]. Imamai (a.s) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba, daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (a.s) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri, bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai a kan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kira ka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambayaâ€‌[2]. Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambayaâ€‌. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirrin samuwarsa da karamarsa, kuma ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuwa yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (a.s) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta, domin kada wahami ya yi galaba a kansa, sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa. Imam Zainul-abidin ya kwadaitar matuka kan wanzuwar izzar musulmi da karfinsu, kwadayin Ahlul Baiti (a.s) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne a matakin Imam Zainul Abidin (a.s) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyakaâ€‌ wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuriâ€‌. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.â€‌ Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsawon addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u, da kuma shirya kansu, da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jihadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa, kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya, da nisantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.
|