Halayen Imam Sajjad (a.s)



Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wacce take sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, da kebewa da shi da sirrinka, da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (s.a.w) da manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunsa, da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wadanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane a kanka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u.

Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda zaka yi hakuri a kan munanan abubuwan da suke faruwa, da kuma yadda zaka yi yayin da kake rashin lafiya, da kuma yayin da kake lafiya lau. Daga cikinsu akwai wadanda suke yi maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a. Abubuwan da suke kunshe cikin addu’ar Imam su ne:

Na farko: Sanin Allah da girman kudurarsa, da bayanin kadaita Shi, da tsarkake shi da mafi zurfin kalmomi na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu’a da salo daban-daban, kamar yayin da kake karantawa a addu’a ta farko: “Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da ya kasance kafin shi, na karshen da babu wani na karshe da zai kasance bayansa, wanda idanuwan masu gani suka gaza ganin sa, wahamce-wahamcen masu siffantawa suka gajiya wajen siffanta Shi, Ya fari halittu da kudurarsa a farkon farawa, ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa.â€‌. Karanta ma’anar na farko da na karshe da kyau da kuma tsarkake Allah (s.w.t) daga kasancewar wani gani ko wahami ya kewaye shi, da kuma tunani kan zurfin ma’anar halittawa da samarwa.

Sannan ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah da tadabburi a cikin addu’a ta 6: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta dare da rana da karfinsa, ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa, ya sanya wa kowanne daga cikinsu iyaka ayyananniya, yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan’uwansa, da kaddarawarsa ga bayi a cikin abin da yake ciyar da su, kuma yake sanya su su girma. Sai ya halitta musu dare domin su huta daga wahalar kaiwa da komowa da dawainiya, kuma ya sanya shi sutura domin su lulluba da hutunsa, sai ya zama wartsakewa da karfi garesu domin su sami jin dadi da sha’awa da shi. Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa’idar halittar rana da dare, da kuma abin da ya kamata mutum ya yi godiyarsa na daga wadannan ni’imomi.

A wani salon kuma na bayanin dukkan al’amura a hannun Allah (s.w.t) suke zaka karanta a addu’a ta 7 cewa: “Ya wanda da Shi ne ake warware kulle-kulle! Ya wanda da shi ne kaifin tsanani yake dakushewa! Ya wanda daga gareShi ake neman mafita zuwa yalwar sauki! mawuyatan al’amura na rusunawa ga kudurarka! sabubba suna tasiri ne da ludufinka, kuma kaddarawarka ta gudana ne a bisa ikonka, abubuwa suna zartuwa da nufinka ne, suna masu umartuwa da nufinka ba tare da fadarka ba, kuma masu tsawatuwa ne da nufinka ba tare da haninka ba.

Na Biyu: Bayani game da falalar Ubangiji ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Ubangiji komai abin da ya yi na da’a da ibada kuwa, da kuma yankewa domin komawa zuwa ga Ubangiji kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 37: “Ya Allah hakika babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka sai wata Kyautatawarka ta same shi wacce zata sake lizimta masa wata godiyar, kuma ba ya kaiwa ga matukar da’arka koda kuwa ya dage sai ya gaza yin yadda ka cancanta ga falalarka, Mafificin mai godiya gareka a bayinka ya gaza a kan godiyarka, kuma mafi bautarsu mai takaitawa ne ga bautarKaâ€‌.

Saboda girman ni’imomin Allah (s.w.t) kan bawansa da ba su da iyaka bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi, yaya kenan idan kuma ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abin da fakara mai zuwa ta addu’a ta 16 take nunawa: “Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta fadi, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage, kuma in yi ruku’u gareka har bayana ya sance, kuma na yi maka sujada har kwayoyin idanuna su faffado, kuma turbayar kasa ta cinye duk tsawon rayuwata, kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen rayuwata, sannan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sannan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga munanan ayyukana baâ€‌.

Na uku: Sanar da lada da azaba, da aljanna da wuta, da kuma cewa ladan Ubangiji dukkaninsa kyauta ne kawai, kuma bawa yana cancantar azaba ne da mafi karancin sabo da ya yi, kuma Ubangiji yana da hujja a kansa game da haka.

Haka nan dukkan addu’o’in Sahifatus Sajjaddiya sun kawo maganar irin wannan azaba mai tasiri, domin tsoratarwa da sanya tsoro a zuciya, da sanya mata sa tsammani da ladan Ubangiji, dukkan wannan shaida ce a kan haka ta salo daban- daban da yake sa wa zuciya tsoro kan sabo. Kamar abin da zaka karanta a addu’a ta 46:- “Hujjarka tabbatacciya, Shugabancinka tsayayye ne ba ya gushewa, don haka tsananin azaba madawwamiya ta tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gareka, tsiyacewa ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, kaikawonsa a cikin ukubarka ya tsawaita, bukatarsa ga burinsa na samun sauki ya nisanta, saukin samun mafitarsa abin yanke kauna ne, adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, hakika ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzuroriâ€‌.

Kuma kamar yadda kake karanta addu’a ta 31: “Ya Allah! ka ji kan kadaitakata ta gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka, da firgicewar gabobina don haibarka, kuma ya Ubangijina! zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a farfajiyarka, idan na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba.â€‌.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next