Halayen Imam Sajjad (a.s)Dukufa Kan Addu’a: Annbin Allah (s.a.w) Ya ce: “Addu’a makamin Mumini ce, kuma jigon Addini ce, kuma hasken sammai da kasa ceâ€‌. Shi ya sa ta zama daga siffofin shi’a da suka kebantu da su, hakika sun wallafa abin da ya kai gomomi na manya da kananan littattafai game da falalarta da ladubbanta, da kuma addu’o’in da aka rawaito daga Ahlul baiti (a.s). Kuma an rabuta abin da manzo da Ahlul Baiti (a.s) suke gurin cim masa na kwadaitarwa a kan yin addu’a a cikin wadannan littattafai. Har ma ya zo daga garesu cewa: “Addu’a ita ce mafifciyar ibadaâ€‌. Da kuma cewa: “Mafi soyuwar aiki a bayan kasa a gun Allah madaukaki ita ce addu’aâ€‌. Kuma ya zo cewa: “Addu’a tana mayar da kaddara da bala’iâ€‌. Da kuma cewa: “Addu’a waraka ce daga dukkan cutaâ€‌.
Kuma ya zo game da Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (a.s) cewa, ya kasance mutum ne ma’abocin addu’a, hakan nan ya kamata shugaban masu Tauhidi kuma shugaban mabiya Ubangiji ya kasance. Kuma addu’o’insa sun zo kamar yadda hudubobinsa suke a matsayin alama daga almomin balagar magana da fasaharta kamar addu’ar Kumail Bn Ziyad wacce ta kunshi ilimin sanin Ubangiji da fuskantarwar Addini, da kuma abin da ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga musulmi na gari. Hakika addu’o’in da suka zo daga Annabi (s.a.w) da Ahlul Baiti (a.s) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi -idan ya yi tunani a kansu- sukan cusa masa karfin imani, da karfin akida, da ruhin sadaukar da kai a tafarkin gaskiya, da sanin kansa, da dadin ganawa da Allah, da yankewa zuwa gareshi, kuma tana lakkana masa abin da ya wajaba a kan mutum ya san shi a addininsa, da kuma abin da yake kusantar da shi zuwa ga Allah Madaukaki, ya kuma nesata shi daga barna da son zuciya da bidi’a batacciya. A takaice dai wadannan addu’o’in sun kunshi sanin Addini ta fuskar kyawawan dabi’u da tsarkake zukata, ta wata fuskar kuma sun kunshi akidar Musulunci, kai ita ce ma mafi girman madogarar ra’ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u. Idan da mutane sun iya kuma ba dukkansu ne masu iyawa ba, da sun shiriyu da shiriyar da wadannan addu’o’in suke kushe da ita a cikin abin da ta kunsa madaukaka, da ba zaka samu irin wannan fasadin da kasa take cike da shi ba, kuma da wadannan rayukan da sharri ya yi musu katutu sun yi shawagi a sammai domin jin gaskiya, sai dai yaya dan Adam zai saurari maganar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya alhalin fadinsa madaukaki ya nuna hakikaninsu da fadinsa: “Hakika rai mai umarni da mummuna ceâ€‌. Surar Yusuf: 53. “Kuma mafi yawancin mutane ko da kayi kwadayi ba masu shiryuwa ba neâ€‌. Surar Yusuf: 103. Na’am abin da ya kawo kafuwa da damfaruwar munanan ayyuka ga mutum shi ne, rudin kansa, da jahiltar munanan ayyukansa, da yaudarar kansa cewa shi yana aikata aikinsa, sai ya yi zalunci ya ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha’awarsa yadda ransa yake so, tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi komai ba sai abin da ya dace ya aikata, kuma ya runtse dagangan daga munin abin da ya aikata, ya kuma karanta kuskurensa a idanunsa. Wadannan addu’o’in daga hadisai da suke samun karfafa daga tushen wahayi, sun yi kokarin sanya mutum ya koyi zargin kansa da kadaita zuwa ga Allah (s.w.t), domin su cusa masa furuci da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne, wanda ya wajaba a kansa ya yanke zuwa ga Ubangijinsa domin neman tuba da gafara. Kamar misalin fadin mai addu’a a cikin Addu’ar Kumail: “Ya Ubangijina! Ya Majibincina! Ashe zaka gudanar da hukunci a kaina a kan abin da na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatarwar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abin da ya so, kuma hukuncinka ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinka saboda abin da ya gudana gare ni na daga hakan, kuma na saba wa wasu daga umarce-umarcen ka.â€‌ Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikrari a cikin jama’a, duk da kuwa yana daga cikin mafi tsananin wahalar halaye ga mutum koda kuwa tsakaninsa ne da ransa. Idan da wannan hali zai samu ga mutum, da ya samu sha’ani mai girma na kamala wajan rage takamar kansa mai sharri, da tarbiyyantar da ita a kan alheri. Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa, to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunani domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar ita ce dukufa a kan karanta wadannan addu’o’in da aka samo daga ruwayoyi, wadanda kuma suke ratsa zuciya, kamar karanta addu’ar Abi Hamza Assumali. “Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarkaâ€‌. Yi tunani a kan wannan kalma “Ka rufe niâ€‌, a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka a kan wannan al’amari, ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan fakara bayan waccan: “Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba, kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubinâ€‌. Wannan irin furuci daga cikin zuciya, da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana, yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (s.w.t) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane, idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu’ar sirri, da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah, ya yi godiya gare shi da ya yi masa afuwa alhalin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa: “Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka, da yafewarka bayan kudurarkaâ€‌. Sannan kuma addu’ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (s.w.t), domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa, yayin da yake cewa: “Kuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka, kuma suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramtaâ€‌. Wannan shi ne tsarin salon addu’ar a ganawa ta asirce ta tsarkake zukata, da saba wa son ransu, da yin da’a, da barin aikata sabo, da wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka alhalin ga su da yawan gaske.
|