Halayen Imam Hasan (a.s)1. Daga cikin wasiyyarsa (a.s) ga wani daga sahabbansa: Ka yi aiki domin duniyarka kamar cewa zaka rayu ne har abada. Kuma ka yi aiki domin lahirarka kamar gobe zaka mutu. Kuma idan ka so daukaka ba tare da dangi ba, da kwarjini ba tare da mulki ba, to ka fita daga sabon Allah zuwa da'arsa (s.w.t), kuma idan wata bukata ta sanya ka abokantakar mutum, to ka abokanci wanda idan ka abokance shi zai haskaka ka. 2. Daga cikin wasiyyarsa ga wani daga 'ya'yansa: Ya kai dana kada ka yi 'yan'uwantaka da wani har sai ka san dabi'unsa. Idan ka samu bayani mai kyau a game da dabi'un nasa kuma ka yarda da abokantakar,… to ka abokance shi a kan zaka yi masa uziri idan ya yi kuskure da kuma taya shi jin zafi da bakin ciki a lokacin da yake cikin tsanani. 3. Daga cikin wa'azozinsa (a.s) ga kowa da kowa: Bayin Allah ku wa'azantu daga abubuwan da suka faru. Kuma ku dauki darasi daga ayyukan wadanda suka gabata. ku hanu daga ni'imomi, kuma ku amfana da nasihohi. Allah ya isa abin riko kuma mai taimako. kuma Kur’ani ya isa abin kafa hujja kuma abokin husuma. Sannan Aljannah ta isa lada. Kuma wuta ta isa azaba kuma ta isa makoma. Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com www.hikima.org Saturday, July 31, 2010 [1] Nisa'i: aya: 86. [2] Manakib: mujalladi 4, shafi: 19. [3] An ce: 28 safar.
|