Halayen Imam Hasan (a.s)Imam Hasan (a.s) ya kasance shi ne wanda manzon Allah ya fi so matuka, ya kasance manzon Allah (s.a.w) yana salla shi kuwa yana yaro ya hau kansa manzon Allah (s.a.w) ya tsawaita sujada saboda kauna da girmamawa gareshi. Imam Hasan (a.s) ya kasance jarumi ne matuka, kuma ya kasance daga wadanda suka fi kowa jarumta a yakokin da aka yi lokacin halifofi domin daukaka musulunci. Hatta da sulhun da ya yi da Mu'awiya bai so shi ba har sai da ya tabbatar da cewa Mu'awiya ya yi amfani da 'yan leken asirinsa da sauran munafukai domin su yada jita-jitar son sulhu da daina yaki, kuma da yawa daga mabiyansa sun samu ruduwa da wannan lamarin, don haka idan ma ya yi yaki jama'arsa zata kasu gidaje daban-daban ne, kuma da yawa wasu ma zasu ki yakin, wasu kuwa ma an riga an ba su kudi don kashe shi a cikin lokacin yakin. Don haka maslaha shi ne ya yi sulhu domin jurewa mafi saukin wahala biyu da za a iya fuskanta, sai ya zami mummuna ya bar mafi muni, wato ya zabi yin sulhu duk da ya san cewa Mu'awiya ba ruwan shi da kiyaye sharuddan addini, maimakon ya yi yaki a kashe duk wadanda suka rage daga wadanda suka yi wa addinin musulunci hidima, hada da shi kansa Hasan (a.s) da dukkan sauran alayen manzon Allah (s.a.w). Bayan dukkan wadannan lamurran ne Imam Hasan (a.s) ya zabi komawa Madina ya assasa makaranta yana yaye dalibai yana aika su garuruwa domin koyar da addini ingantacce da kakansa ya zo da shi ga wurin ubangiji madaukaki domin shiryar da talikai. Da haka ne ya yaki jahiliyayyar da ake yadawa a Sham ga mutane da sunan addini, da wannan ne kuma zamu gane cewa yakin Imam Ali (a.s) da Mu'awiya yaki ne da ya fara tuntuni tsakanin gaskiyar Banu Hashim da karyar Banu Umayaya la'anannu. Sai ya kasance ci gaban yaki ne tsakanin shiriya da bata, da gaskiya da karya, da gyara da barna; Abdusshams, da Harbu da Abusufyan, da Mu'awiya, da Yazid sun tsaya a bangaren barna da bata da karya, suka yaki Abdulmudallib, da Abu Dalib, da Manzon Allah (s.a.w) da Ali da Hasan da Husain (a.s) wadanda suka tsaya a bangaren gyara da shiriya da gaskiya. Imam Hasan Mujtaba (a.s), shi ne Hasan dan Ali dan Abu Dalib (a.s) kuma babarsa Fadima Zahra 'yar Muhammad (s.a.w) jikan Manzon Allah (s.a.w) mafi girma kuma na biyu a halifofinsa kuma Imami jagora ga mutane bayan babansa (a.s). An haife shi a Madina mai haske ranar talata a rabin watan Ramadan a shekara ta uku hijira, kuma ya yi shahad da guba da Mu'awiya dan Abu Sufyan ya yi masa kaidinta ta hannun matarsa Ja'ada 'yar ash'as wannan kuwa a ranar alhamis bakwai ga watan safar[3], shekara ta hamsin hijira, kuma dan'uwansa Imam Husain (a.s) shi ne ya yi masa wanka ya binne shi a Bakiyya a Madina inda kabarinsa yake yanzu wanda abin takaici wahabiyawa suka rushe kubbarsa. Imam Hasan (a.s) ya rayu a karkashin Inuwar kakansa manzon Allah (s.a.w) kuma a cikin kulawar mahaifiyarsa Fadimatu Azzahra’u (a.s) shekaru bakwai. Kuma ya rayu tare da mahaifinsa (a.s) har ya zuwa rasuwarsa a shekara ta (40 bayan hijira). Kuma wannan lokacin wanda ya rayu a cikinsa tare da kakansa da mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya tara masa dukkan abubuwa na tarbiyyar Musulunci mai kaiwa ga gaci. Sai ya zamana ta samar da mutum musulmi Kamili mai tsarkin zuciya.
|