Halayen Imam Hasan (a.s)Sannan kuma al'ummar musulmi sun samu an cakuda musu ta yadda ba sa iya gane gaskiya da karya, sai ya kasance sun dauka domin mulki ne ake yin yaki, ga mabarnata sun ci galaba kan na gari sakamakon mutane suna son barna da son rai, domin karkatar da dukiyar kasa zuwa ga wasu tsuraru, da neman kin tsayar da adalci a zaman tare, da tattalin arziki, da siyasar al'umma da sauransu. Gurbacewar al'umma ce ta sanya su ganin Imam Ali (a.s) a wannan zamani kamar wani mutum da ba shi da wayo, don haka ne suka ce Imam Ali mutum mai jarunta sai dai ba shi da wayo. Imam Ali (a.s) ya yi raddi mai kaushi a kan wadannan mutune da cewa: Wallahi Mu'awiya bai fi ni wayo ba, sai dai yaudara ce da fajirci yake yi, kuma ba don kin yaudara ba, da na kasance mafi iya yaudarar mutane. Sai dai dukkan yaudara fajirci ne, dukkan fajirci kafirci ne, dukkan mayaudari yana da tutar wuta da za a san shi da ita ranar kiyama. Mutane sun kasance suna son san rai ne, don haka sai suka bi jagororin kabilunsu da makamantansu, sai suka dulmuyar da su domin neman abin duniya. Mu'awiya ya kasance ya sayi dukkan jagororin kabilu domin su bi duk abin da yake so, sannan ya sayi dukkan kwamandojin yaki mabiya son rai, da haka ne ya sayi hatta da wasu daga makusantan Imam Hasan (a.s) kamar Ubaidullah dan Abbas saboda kudi da suka kai dirhami miliyan daya. Muna iya ganin misalign wannan lalacewa ta mutane da ta kai ga Imam Husain (a.s) ya aika Muslmi dan Akili Kufa amma sai dan Ziyad ya yi musu alkawarin dukiya da kudi da zai ba su, sai suka waste suka bar Muslim shi kadai!. Misalin irin wadannan lamurran suna da yawa matuka a tarihin Imam Hasan (a.s) da Imam Husain (a.s) kuma muna iya ganin yadda hatta da matar Imam Hasan (a.s) ta kashe shi saboda kawai Mu'awiya ya yi mata alkawarin kudi masu yawa, da kuma auren dansa Yazid tsinanne. Muna ganin Imam Ali (a.s) ya gaji da wannan al'ummar har sai dai ya yi mata addu'ar Allah ya raba shi da ita, ya raba su da shi. Yana mai cewa: Ya ubangiji na gaji da su, sun gaji da ni, ka hutar da ni su, ka hutar da su ni. Muna ganin bayan mutuwar Imam Ali (a.s) yadda mutane suka zo wurin Imam Hasan (a.s) suka yi masa bai'a a kan shi ne halifan babansa kamar yadda babansa ya yi wasiyya, suka ce; kai ne wasiyyin babanka kuma halifansa, mu masu ji ne daga gareka, ka ba mu umarninka. Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: Kun yi karya, wallahi ba ku cika alkawari ga wanda ya fi ni ba, yaya kuwa zaku cika shi gareni!. Yaya kuwa zan samu nutsuwa da ku ban aminta da ku ba? Idan kuwa kun kasance masu gaskiya to alkawarinmu da ku shi ne wurin rundunar garin Mada'in, sai suka tafi can kuwa. Shin Imam Hasan (a.s) wanda yake shi ma'asumi ne zai yi siyasar yaudara irin ta Mu'awiya ko kuwa irin ta babansa! Sai dai kowa ya sani cewa Imam Hasan (a.s) ba yadda za a yi ya yi siyasar mayaudara fajirai, don haka ne ba zai raba dukiya a tsakanin rundunarsa ba bisa son rai, wannan kuwa yana nufin su sake yaudararsa kamar yadda suka yaudari babansa (a.s). Wannan lamarin ne ya tilasta shi barin jagoranci domin yanzu jagoranci ya koma wuri ne mai dauda maras tsafta, wuri ne mai kazanta da yanzu kuma ba wani abu ne da za a iya amfani da shi domin hidimar musulmi da musulunci ba.
|