Halayen Imam Hasan (a.s)An ba shi halifanci bayan rasuwar mahaifinsa (a.s) a shekara ta (40 bayan hijra). Kuma daga cikin muhimman ayyukan da ya yi a lokacin da ya karbi halifanci: Tura mayakan mahaifinsa (a.s) wadanda ya riga ya tanade su domin yakar Mu’awiya dan Abu Sufyan saboda ya bijire wa umarnin Imam Ali (a.s) na cire shi da ya yi daga gwamnan Sham. Kuma ya kauce daga koyarwar Musulunci da hukunce-hukuncensa a cikin fagagen shugabancinsa a matsayinsa na gwamna a Sham… Sai dai cewa wasu dalilai sun hana Imam Ali (a.s) kawar da Mu’awiya ta hanyar yin amfani da wadannan mayaka. Muhimman wadannan dalilai su ne: 1. Ha’incin jagoran mayakan a sakamakon rudin da Mu’awiya ya yi masa na bayar da dukiya da kuma burace buracen samun abin duniya. 2. Rarrabuwar kan mayakan ta hanyar masu haifar da fitina daga cikin mutanen Mu’awiya. 3. Kasantuwar akwai khawarijawa a cikin mayakan, ta yadda suka yi amfani da wannan damar suka shiga rarraba kan mayakan da tarwatsa su. Bayan rarrabuwar kan mayakan Imam Hasan (a.s) da watsewar su, sai yanayin siyasa a wancan lokacin ya saka Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu’awiya kuma ya koma zaman lafiya… Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu’awiya a bisa wasu sharudda, muhimmai daga cikinsu su ne: 1. Imam Hasan (a.s) zai ba wa Mu’awiya halifanci a bisa sharadin cewa Mu’awiya zai yi aiki da littafin Allah da kuma sunnar manzon Allah (s.a.w) da rayuwar halifofi salihai.
|