Halayen Imam Hasan (a.s)2. Halifanci zai koma hannun Imam Hasan bayan Mu’awiya idan Imam Hasan yana raye. Idan kuma ya rasu to zai bayar da halifanci ga dan'uwansa Imam Husain (a.s). Kuma bai halatta ba Mu’awiya ya yi wasicin halifancin ga wani. Sai dai cewar Mu’awiya a lokacin da ya gama kame halifancin nan bai cika sharuddan ba sai ya yi ha’inci. Muhimman abubuwan da suka jawo sulhun su ne: 1. Kaskantar Irakawa a gurin mutanen Mu’awiya wadanda suke yakar su a lokacin Imam Hasan (a.s) domin su bar taimakon sa (a.s) a lokacin da yake kiran su zuwa ga mayar da martanin wannan dakarun na yaki. 2. Nisantar manyan mutane masu yawa daga Imam Hasan (a.s) daga cikin wadanda suka yi masa bai’a saboda kwadayin mukami da ganima. Hakan kuwa saboda lazimtar Imam Hasan (a.s) ga wadatuwa da kuma amana wajen bayar da aiki, da daidaitawa wajen rabon dukiyar haraji, domin aiki da adalcin Musulunci. 3. Shigar munafukai daga cikin masu leken asiri na Mu’awiya da ma’aikatansa cikin mutanen Imam Hasan (a.s) domin kawo rarrabuwa da batarwa. 4. Kin fitowar da yawa daga cikin wadanda suka yi wa Imam Hasan (a.s) bai’a daga cikin Irakawa a kan yakar Mu’awiya, zuwa jihadi tare da shi (Imam Hasan) saboda yaudara. 5. Yada wasikun da Mu’awiya ya yi, wadanda suka zo masa daga gurin Irakawa, wasikun da suka kunshi biyayya ga Mu’awiya da yin ha'inci ga Imam Hasan (a.s) a tsakanin daidaikun mayakansa, domin raunana rundinar mayakansa da gwaurayata, da kuma cakuda ta. Imam Hasan (a.s) ya rasu a Madina a shekara ta 50 bayan hijira. Daga cikin shiryarwarsa:
|