Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Raja’a nau’i ce na tayar da matattu da jikkunansu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili a kan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili a kan cewa dole ta zama abin mamaki, sai dai kawai mu ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. A ce masa: “wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu” Yasin: 78-79.

Dalilinmu a kan Raja’a kuwa su ne nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Kur’ani, kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta rayar da matattu: “Kuma Ina warkar da wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49.

Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai rayar da wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259.

Da kuma ayar da take cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11.

Ma’anar wannan ayar ba za ta yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba, duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba, kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba. Sannan hadisan Ahlul Baiti (A.S) mutawatirai sun zo game da tabbatar raja’a a cikin wannan al’umma kamar yadda ta faru a al’ummun da suka gabata.

Suka da Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam ya yi na cewa; “Yahudanci ya bayyana a cikin shi’anci ta hanyar imani da Raja’a” ba shi wani asasi, domin idan haka ne Raja’a ta zo a kur’ani mai girma sai ya ce da mu; Yahudanci ma ya bayyana a Kur’ani saboda batun Raja’a”.

Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita, kuma aukuwarta ba mustahili ba ne.

 

Menene Hakikanin Hukunce-hukuncen Addini?

Hukunce-hukuncen addini su ne tattararrun dokokin shari'a da suke kunshe cikin umarnin Allah da haninsa, da suka hada da wajibai da haram, da mustahabbai da makaruhai da sauransu, wadanda ubangiji madaukaki ya sanya su daidai da maslaha da alheri ga bayinsa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi mustahabbi garemu.

Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Amma wasu daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.

Abin da yake ingantacce shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa[20].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next