Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Tambaya Da Amsa Game Da Akida

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma lalle, hakika mun ba wa Lukman (A.S) hikima. (Muka ce masa): Ka gode wa Allah, kuma wanda ya gode yana godewa ne domin kansa.[1].

    Gabatarwar Mawallafi

 Tun bayan wafatin manzon Allah (S.A.W) al’ummar musulmi ta fada cikin rarraba da sabani, kuma mazhabar Ahlul Baiti (A.S) karkashin jagorancin imam Ali (A.S) da mabiyansa har zuwa wannan rana tare da taimakon manyan malaman addinin musulunci masu daraja sun shagaltu da bayyanawa da kuma sharhin aikidoji ingantattu.

Mafi girman matsalar isar da sakon wannan mazhaba a tsawon karnonin da suka gabata ita ce samuwar masu sabawa, ko makiya wannan mazhaba ta Ahlul Bait (A.S) da suka dukufa wajan kage da karya a kan wannan mazhaba ta hanyoyi da dama, kamar kafafen watsa labarai da kuma rubuce-rubuce na kage, da sharri, da karya da ba sa dogara da tsamowa daga littattafan koyarwar mazhabar.

Dadin takaici sai wasu 'yan kanzagi da rikicin siyasar hukumomin da suka gabata na halifanci kamar Umayyawa da Abbasawa da Usmaniyawa da su sun yi wannan ne domin kare mulkinsu ta hanyar kage ga shi'a mabiya Ahlul Bait (A.S), su ma suka dauka, har suka fi mai kora shafawa, suka zarce gona da iri, musamman a wannan zamani namu da muke ciki.

Ta haka ne ake ta jifan wannan mazhaba da tuhumomi marasa ma’ana da kan gado iri-iri da ake danganta su ga wannan mazhaba, daga cikin irin wannan tuhumomi da kage da ake yi a kan shi’a akwai maganar gurbata da jirkita da canja kur’ani, da auren mutu’a, ko yadda ake yin alwala da salla, da Isma, da Raja’a, da Bada.

Abin takaici saboda rufewar ido da son kai, sai aka gafala daga wannan mafi kyawun hanyar, domin sanin kowace mazhaba ita ce komawa zuwa ga littattafan wannan mazhaba, da maganganun malamanta da masananta, da kuma komawa zuwa ga littattafan su, kuma komawa wasunsu domin saninta yana daga cikin mafi girman kuskure da rashin adalci da, in ban da sabani da jayayya babu wani abin da za a samu daga hakan.

Saboda haka mafi kyawun hanya ita ce hanyar hankali ingantacciya ta sanin mazhabar Ahlul Bait (A.S) ta hanyar komawa zuwa ga littattafansu.

 Wadannan abubuwa ne da aka yi bayaninsu a hankalce da dalilai masu gamsarwa daga Kur'ani da Sunnar Annabi (S.A.W), sai na ga ya dace in dan yi wata karamar mukaddima a game da hakan da surar tambaya da amsa, domin matashiya game da dan kadan daga bayanai game da akidojin Mazhabar Ahlul Bait (A.S).

Da yake ranar kammalawa ta yi daidai da ranar wafatin Ummulmuminin Khadijatul Kubra (A.S) don haka ina rokon Allah ya sanya ladan rubutun gareta ya kuma haskaka kabarinta da shi, sa’annan mun sanya shi tambayoyi 34, domin neman gafarar Allah da adadin shekarun mawallafin.

Hafiz Muhammad Sa'id Kano Nigeria



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next