Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Kuma wajibi ne a girmama Kur’ani mai girma da daukaka shi a cikin magana ko a aiki, bai halatta ba a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda ake dauka cewa ita yanki ce daga cikinsa.

Kamar yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya taba kalmominsa ko harrufansa; “Babu mai shafarsa sai wadanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79.

Shin sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba, ko haila, ko jinin biki, da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne, sai dai idan sun yi wanka ko alwala kamar yadda bayani ya zo dalla-dalla a cikin littattafan fikihu.

Haka nan bai halatta ba a kona shi ko wulakanta shi ta kowace fuska da abin da yake wulakanci ne a ganin mutane, kamar jefar da shi, ko sanya masa kazanta, ko shurinsa da kafa, ko sanya shi a wuri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan, ko tozarta shi, da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu, to shi yana daga cikin masu karyata Addinin Musulunci da alamominsa masu tsarki, kuma shi abin hukuntawa ne da fita daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

Menene Matsayin Musulunci Da Sauran Shari’o’i?

   Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin musulunci zamu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dawwamammiya wato Kur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.

 Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci, ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu, ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan suke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata, su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da yake hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawan, kamar Attaura da Injila, da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya, kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba. Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata, domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci, to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi.

Duk wanda ya tashi a Addinin yahudanci ko kuma kiristanci, shi Bayahude imaninsa da addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken addinin kiristanci da addinin musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu ba, mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba, haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa[44].

Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci, ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi

Amma musulmi idan har ya yi imani da musulunci, to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar musulunci, don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne, saboda annabin musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi mai gaskiya ne Amintacce, “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4.

Yana wajaba a kan musulmi saboda sabanin mazhabobi da ra’ayoyi, da kuma samuwar kungiyoyi, ya yi bincike, ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a, domin bai halatta gare shi ba ya bi ra’ayin iyaye ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa suke a kai ba, babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T), domin a nan babu wani boye-boye ko sassauci, ko bangaranci. Dole ne ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da yake kansa tsakaninsa da Allah, ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah[45].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next