Tambayoyi Da Amsoshin Akida Friday: 10 Ramadan 1426 14 October 2005 22 Mihir 1384 Shin Ya Halatta A Yi Koyi Da Wani A Usuluddin?
Ba ya inganta ba a yi koyi da wani a cikin shika-shikan addini da aka san su da Usuluddin, don haka abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yancin hankali. Don haka ya wajaba a kan mutum mai hankali ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari a kan asasin shika-shikan akidarsa wadanda suka hada da : 1. Kadaita Allah 2. Annabci 3. Imamanci 4. Tashin kiyama Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya kauce wa tafarki madaidaici, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada[2].
|