Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Daga cikin siffofin da suka koru ga ubangiji da akwai jiki, da sura, da motsi, ko rashin motsi, da nauyi, ko rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa.

Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, kamar a misali idan aka ce mai ilimi yana nufin ba jahili ba ne, wanda wannan yakan kai ga kore siffofin kamala ga Allah (S.W.T)[10].

Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, wanda wannan yakan kai ga kididdigar zatin Allah da rashin kadaitakarsa da samuwar ababan tarayya[11] gareshi.

Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:

Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[12], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, Wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[13].

Menene Adalcin Allah?

Adalci yana daga siffofin Allah madaukaki na kamala wadanda suke tabbatattu kuma na aiki, abin da ake nufi shi ne; Allah madaukaki ba azzalumi ba ne, ba ya take hakki a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hakkin hukunta masu sabo, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta.

Kuma Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau, kuma ba ya aikata mummuna saboda shi mai iko ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarsa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan aiki da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.

Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu ba:

 1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.

2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next