TSari Da Kayyade Iyali



Na uku; Wasu jama’a sun tafi a kan haramta Kayyade iyali kamar Muhammad Dan Habban Al-Basti Mai littafin Assahih Wattasanif shafi na 154[7]. Da Ibn Hazam Al-Andulusi suna cewa: Kayyadewar daidai take da zubar da ruwa mai kwarara daga wajansa alhalin filin shuka yana bukatarsa kuma a shirye yake da ya karbe shi domin fitowar tsiro da ‘ya’yan itace na daga abin da yake amfanar mutane da raya halittu da samammu gaba daya.

Amsa ita ce; wannan duk abin da suka fada ba ya sanya kayyade iyali ya zama haram, na’am yana iya zama karahiya idan da yin sa zai haifar da wani abu kamar rashin tsari a al’umma da makamancinsa, hada da cewa sun yi kiyasin farji da gona, mutum da shuka, ruwa kuwa da mani, alhali akwai bambanci mai nisa tsakanin wadannan abubuwan biyu.

Saboda haka bisa abin da aka ambata Kayyade Iyali ko tsara su a kan kansa halal ne, kuma suna iya zama wajibi a wani lokaci, amma mun riga mun gabatar da cewa Kayyade Iyali da ma’anar dakatar da samar da dan Adam gaba daya har zuwa wani lokaci ko ma ya kare wannan haramun ne ba mai halatta shi.

Hukuncin Zubar Da Ciki

Kamar yadda muka kawo, cikin hanyoyin da ake amfani da su domin Kayyade Iyali akwai zubar da ciki, mu sani cewa malaman musulunci gaba daya babu sabani sun tafi a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai domin wannan kisan kai ne da kuma kashe mai rai, kamar yadda duk sun tafi a kan haramcin yin hakan matukar zai kai ga mutuwar uwar ko da ko rai bai shige shi ba.

Daga cikin dalilai a kan haka shi ne; Haramcin jefa rai cikin halaka da kuma wajabcin kare rai mai alfarma da daraja kamar ran mutum. Amma an yi sabani idan ba a busa masa rai ba wato bai kai wata hudu ba kuma uwa ba zata cutu ba. Fatawar malaman mazhabar Ahlul Bait wato Shi'a yin hakan haramun ne a shari’a koda kuwa yanzu ya shiga[8], sannan akwai wajabcin biyan diyya kamar haka:

1.      Idan maniyyi ne dinare ishirin

2.      Idan gudan jini ne dinare arba’in

3.      Idan tsoka ce dinare sittin

4.      Idan kashi ne dinare tamanin

5.      Idan an tufatar da kashin nama dinare dari



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next