TSari Da Kayyade Iyali



A kusan karni na sha tara Faransa ta fuskanci karancin haihuwa matuka sosai. A shekarar 1860 kusan kwata na mutanen Ingila da Wales suna da ‘ya’ya takwas ko tara, amma a kusan 1925 rabin mutanen wannan yanki kowane mutum yana da da daya ne ko ‘ya’ya biyu, kashi daya cikin shida kuwa na mutanen ba shi da da ko daya. Kamar yadda a 1830 a kasar Amurka daduwar farar fata da yawan haihuwarsu yana kashi hamsin 50 cikin dari ne a kowane mutum dubu, amma a shekarar 1930 daduwar ta koma kashi 18 ne kawai. A Ingila, a shekara 1910 kashi 15 suke Kayyade Iyali, amma a shekarar 1935-39 kusan kashi 66 suke bin tsarin Kayyade Iyali. Haka nan a Amurka a 1982 kashi 67.9 ne suke bin tsarin Kayyade Iyali na ma’auratan da suke da shekaru daga 15 – 44, yayin da wasu kashi 14 kuma suke neman haihuwa. Koda yake akwai kabilanci da tasirin Addini da suke kashe kaifin abin, shi ya sa ma kusan kashi 69.6 na farar fata da kuma kashi 61 na Bakar fata suke bin tsarin Kayyade Iyali.

Amma a kasashe masu tasowa abin ya kama ne kamar wutar daji, misali a kasar Tailan kashi 15 ne suke aiki da wannan tsari na Kayyade Iyali a shekarar 1970 amma a shekarar 1981 kashi 60 suke aiki da shi. A Meksiko kuwa a shekarar 1976 ya tashi daga kashi 30 zuwa kashi 40 a shekarun 1980s, kamar yadda a kasar Bangaladish a shekarar 1975 ya tashi daga kashi 8 zuwa kashi 20 a shekarar 1984.

Muna iya cewa dalilai da yawa sukan sanya Kayyade iyali a duniya kamar na Siyasa, da Tattalin arziki, amma akwai karancin cin nasarar gudanar da shi a kasashen da ba su dauki Tsarin Iyali da muhimmanci ba.

Zamantakewa Da Siyasar Kayyade Iyali

A shekarar 1798 Thomas Malthus ya rubuta littafi Mai taken “Asasin al'umma” yana mai nuni da jinkirin yin aure, da kame kai daga saduwa, a matsayin hanyoyin Kayyade Iyali, haka nan a kawai masana a karni na 19 daga masu bincike kamar Jeremy Bentham, Francis Place (Wanda yana da 'ya'ya goma sha biyar), da John Stuart Mill, wadanda suka yi nuni da kwadaitarwa kan hanyoyin Kayyade Iyali a aikace. Robert Dale Owen, dan mutumin da ya kawo canjin zamantakewar al'umma a Skotland, ya taimaka wajan yaduwar wannan tunani a Arewacin Amurka, kuma a shekarar 1832 Charles Knowlton, ya rubuta littafin da aka fi sani da “The Fruits of Philosophy” ko “The Pribate Companion of Young Married People” Wanda a kan haka aka sanya shi gidan sarka, Littafin ya sake bayyana a kasuwannin Ingila bayan shekara biyu da faruwar haka har zuwa shekara hamsin. A shekarar 1876 ne aka daure mawallafi Bristol saboda sayar da littafin, wadannan kame-kame da ya yadu a jaridun Ingila ya sanya jan hankalin mutane zuwa ga Kayyade Iyali da yaduwarsa cikin matsakaita da talakawan al'ummar Biritaniya domin su kyautata rayuwarsu, abin da ya jawo karyewar dokar hana Kayyade iyali gaba daya.

Amma akwai wasu mata biyu da aka sani da Margaret Sanger a kasar Amurka da Marie Stopes a Biritaniya wadanda suka yi kokarin sanya Kayyade iyali ya zama al'marin kasarsu da ma duniya gaba daya, dukkkaninsu sun yi amfani da rikece-rikice da suka mamaye matsalar Kayyade Iyali a matsayin hanyar jawo hankalin mutane zuwa gareshi. Malama Sanger likiciya, ta shiga mawuyacin hali a kan hakan, an ce wannan ya yi mata tasiri saboda ganin mawuyacin halin da mata sukan samu kansu a kai ne yayin haihuwa, sai ta ga yana da kyau mata su hutar da kansu su kayyade haihuwarsu.

 A shekarar 1914 ta fara buga wata mujalla mai suna “The Woman Rebel” domin nuna rashin yarda ga dokokin hana Kayyade Iyali, an rike ta da wannan a matsayin laifi, wanda hakan ya sa ta gudu zuwa kasashen turai, amma ta dawo a shekara 1916 bayan an janye tuhumar daga kanta. Bayan haka ne ta bude Asibitin Kayyade Iyali a garin Brownsbille da Brooklyn da New York, amma 'yan sanda suka kulle Asibitocin da gaggawa, kuma aka kama ita Sanger a matsayin wanda yake neman bata tunanin al'umma, sai dai bayan cece-kuce da samuwar canji an bayar da izinin bude Asibitocin, sannan likitoci suka samu izinin yada wa da bayanin Kayyade iyali ga mutane a Amurka.

Marie Stopes 'yar kasar Ingila; Ita ce mace ta farko da ta fara samun matsayin Dakta a Ilimin Shuke-shuke a Jami’ar Munich a shekarar 1904. A shekarar 1918 ta rubuta wani littafin “Married Lobe” da aka tuhume shi da littafin shakiyanci. Margaret Sanger ta hadu da Marie Stopes ta kuma kwadaitar da ita a kan ta ci gaba da rubuce-rubucenta. Harkar motsi na kawo canji da tsarin Kayyade iyali a Biritaniya daga karshe ya samu jagoranci daga Marie Stopes, wacce tana daga iyali ne masu matsakaicin hali.

Yayin da Sanger take karfafa Kayyade Iyali saboda talauci, da yawan al'umma, da kuma nemar wa mata saukin fadawa hatsarin abin da ciki kan iya jawo musu domin su sami sauki da hutu daga wahala, sai ga shi a shekarar 1918 bayan ta yi aure ba da jimawa ba ta zama uwar 'ya'ya, a kuma shekarar 1922 ta tsayar da kungiyar da ta kafa ta cibiyar Kayyade iyali da aka fi sani da “The Society for Constructibe Birth Control and Racial Progress”[3].

Wasu Bayanai Kan Kayyade Iyali



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next