TSari Da Kayyade Iyali



Shimfida

Tsarin Iyali: Aiki ne na zabi ta wasu hanyoyi na musamman wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba domin rage ko tsayar da haihuwa da yaduwar dan Adam. Hanyoyin sukan hada da daina saduwa, ko zubar da ciki, ko kashe yiwuwar haihuwa, ko bayar da tazara. Wasu suna ganin: Tsarin Iyali wani aiki ne da yakan bayar da dama ga mutum ya kayyade Iyalinsa ko tsara su domin taimaka wa ga warware matsalolin duniya da warwararsu ta dogara kan hakan, amma a wasu lokutan gwamnatocin kasashe ne sukan dauki alhakin gudanar da shi ga al’ummunsu, ya zama doka a kasa.

Farkon motsi a Duniya domin kawo Tsarin Iyali ya fara ne da daidaikun mutane da kungiyoyi, kuma a wannan lokuta ya fuskanci kakkausan suka daga cibiyoyi daban-daban, Mrs Sanger ta yi kokarin samar da cibiyar Tsarin Iyali a Amurka a 1921, Kamar yadda a kasar Ingila aka bubbude cibiyoyin Tsarin iyali. Ba zamu manta da taron shekara ta 1881 wanda cibiyar nan ta Biritaniya ta kira kasashe 40 domin tattaunawa kan batun Tsara Iyali ba, wanda bayan babban taron da aka yi ne aka fara bude irin wadannan cibiyoyi a kasashe da dama.

A Indiya an bude Asibiti na farko domin Tsarin Iyali a 1930 da kuma Bombay a 1925, kamar yadda Margaret Sanger ta yi kokarin samar da kungiyar nan da a yanzu ita ce ta zama Cibiyar tsara iyali ta iyaye ta duniya da aka fi sani da “International Planned Parenthood Federation”.

Kamar yadda aka samu motsi mai karfi domin kayyade iyali a duniya daga shekarar 1960. Lokacin da gwamnatoci suka fara goyon bayan tsarin nan na IPPF. A kasar Amurka William Draper ya karfafa shirin wanda daga karshe ya jawo kafa hanyar bude “United Nations Fund for Population Actibities” a shekarar 1969. Kamar yadda bayan haka tarurruka a kai a kai ba kakkautawa suka yi ta biyo baya, kamar Taron Majalisar Dinkin Duniya a Bucharest a 1974 da a Meksico City a 1984[2].

Kayyade Iyali A Karni Na Sha Tara

A karni na sha tara aka sanya dokoki na halarcin Kayyade Iyali amma ya fuskanci kakkausan suka daga bangarori da dama, a kan haka ne ma aka shelanta dokar halarcin haka ga iyaye a Tehran a 1968 da cewa: Iyaye suna da ‘yancin su Kayyade Iyalinsu ko tsara su. Amma a Jamus ‘Yan Nazi suna ganin wayo ne na kayyade su a matsayin su na jini mafi tsarki a cikin al’ummu. Kuma wannan doka ta halarcin Kayyade Iyali ita ce aka rubuta a Kwansitushen din kasar Yogoslabiya.

A Kasar Sin sun sanya shi a matsayin doka ce ta tilas a kan kowa, amma kotun kasar Amurka ta halatta haka ga kowane mutum ne bisa zabin kansa. Ta wani bangaren kuma Kotun Kasar Singafo (Singapore) ta sanya haraji kan duk wasu iyaye da suke da ‘ya’ya uku ko sama da haka domin tilasta mutane karbar tsarin bisa tilas.

Game da hanyoyin da ake bi wajan Kayyade Iyali, a karshen karni na sha tara kusan kowace kasa ta duniya ta gabatar da dokar haramcin zubar da ciki, amma a yau kusan kashi saba’in na kasashen Duniya sun halatta Kayyade Iyali ta hanyar zubar da ciki, Kasar tarayyar Sobiyot Rasha ita ce farkon kasa a karni na ishirin a (1920) da ta yadda da dokar. A kusan 1960s ne kasashen Turai ta gabas suka amince da hakan.

A Biritaniya ma an sake bibiyar dokar nan ta hukuncin zubar da ciki a shekarar 1967. Haka nan kasashe da dama kamar Indiya, Kasar Sin (China), Australia, Italy, France, Netherlands, da sauran kasashe masu yawa suka bayar da damar hakan ga wanda ya ga dama. A Kasar jamus ‘Yan Nazi suna ganin Kayyade Iyali a matsayin wani zagon kasa ne domin neman rage yawan jini mafi tsarki na Jamusawa, har ma aka zartar da hukuncin kotu a kan wata mata a 1942 a yankin da Jamus ta mamaye na Faransa domin ta zubar da cikin Bajamuse. A shekarar 1943 gwamnatin Third Reich ta zartar da hukuncin kisa kan masu gudanar da zubar da ciki, amma a 1973 a Kasar Amurka aka samu rushewar dokar nan da ta hana zubar da ciki gaba daya. Dangane da Kiristanci a littafin Baibul a (Genesis 38:8-10) Allah ya yi wa Onan ukuba ne ta hanyar daukar ransa saboda yana Azalu, al'amarin da yake nuni da haramcinsa a Kiristance.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next