TSari Da Kayyade Iyali



Hanyar zubar da ciki hanya ce da ake amfani da ita wacce ta shahara tun karni na sha tara. Akwai wasu masana da suka bayar da gudummuwa wajan samar da hanyoyi daban-daban na kayyade iyali kamar; Adam Raciborski, likita a Faransa a 1843, da Hermann Knaus a Austria a 1929, da kuma Kyusaku Ogino a Japan a 1930. Amma game da Afrika a binciken da na yi ban sami wani bincike kwakkwara da aka rubuta game da kayyade iyali a yankin Afrika da tarihinsa ba kamar yadda yake game da Asia mai nisa. Da akwai kuma wani nau’in kayyade iyali da ya shahara a zamnin da a yankin Jaziratul-Arab na binne ‘ya’ya mata da ransu don tsoron talauci ko tsoron kada a ribace su a yaki.

Tsara Iyali Ko Kayyade Iyali

Tsara Iyali shi ne: Tsara haihuwar matan da suke saurin daukar ciki, da kuma marasa lafiya rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka musu wajan warware matsalarsu kuma kawo ‘ya’ya duniya zai kara matsalar ne kawai, wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa kuma ba a kansa ba ne duniya take cece-kuce.

Amma kayyade iyali: Shi ma ya kasu kashi biyu ne; Kayyade Iyali da ya shafi mutum daya da gidansa, da kuma kayyade yaduwar nau’in dan Adam a duniya da takaita yawaitar mutum a duniya ta hanyar kafa wata doka da zata hana yaduwar dan Adam da yawaitarsa da kayyade yawan dan Adam. Wannan kashi na biyu shi ne abin da ake jayayya a kansa, kuma dukkan wannan yana bayani ne kan Tsara Iyali ko iyakancewa.

Hanyoyin Kayyade Ko Tsara Iyali

 Kafin bayanin Shari’ar musulunci da matakinta kan Tsara Iyali ba makawa mu yi bayani game da hanyoyin da mutane suke dauka wajan kayyade ko tsara iyali wadanda sun hada da:-

1-Zubar da ciki: Wannan ita ce hanyar da ake dauka a mafi yawancin kasashe wato zubar da ciki ta hanyar shan kwayoyi ko wata hanyar daban.

2- Azalu: Shi ne mutum ya kauce daga matarsa yayin kwanciya ya fitar da ruwan wajan farjinta yayin kawowa, daga cikin wani nau’i na Azalu a wannan zamani shi ne yin amfani da kwandom wato Robar da zata hana mani shiga farji.

3- Jinkirta aure: shi ne kin yin aure da wuri domin kada a haihu har sai mace ta kusa tsufa ta manyanta tana mai shekaru masu yawa ta yadda da ta fara haihuwa shekarun da zata bar haihuwa zasu riske ta da wuri, Wannan ita ce hanyar da aka fi amfani da ita a Kasar Sin (Cana)

 4- Daina jima’i da mata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next