Hukunce-hukuncen Soyayyae- Makwadaici
275. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: dukkan abotar da kwadayi ne ya kawo ta, to yanke kauna zai warware ta kuwa[49]. 276. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Duk wanda ya yi abota da kai saboda wani abu, to zai juya yayin da ya kare[50]. f- Jahili
277. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kaunar jahilai tana kawo canjin halaye, kuma ta kusa tafiya (wato ba ta dawwama)[51]. 278. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: duk wanda ya yi kauna da wawa, to ya bayyanar da wautarsa[52]. g- Wawa
279. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: son wawaye yana gushewa kamar yadda tururi yake gushewa, kuma yana bari kamar yadda kuraye suke barin (wuri)[53]. 280. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Abotakar wawaye kamar itacen wuta ne, da sashenta yake cin sashe[54]. 281. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: na hana ka abota da wawa, domin shi yana cutar da kai ta yadda yake ganin cewa yana amfanarka ne, kuma yana munana maka ta yadda yake ganin yana faranta maka ne[55]. h- Sarakuna
282. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: da kyar ne kaunar sarakuna da maha’inta take dawwama(ga mutum)[56]. i- Mashayin giya
283. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Kada ku gaskata mashayin giya; domin abotarsa nadama ce[57]. j- Maras cika alkawari
284. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kada ka dogara kan kaunar wanda ba ya cika alkawarinsa[58].
|