Hukunce-hukuncen Soyayya



Wanda Sonsa Yake Mustahabbi Ne

A- Muminai

239. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Son mumini ga mumini saboda Allah yana daga mafi girman rassan imani[6].

b- Malamai

240. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ka wayi gari malami, komai neman ilimi, ko mai jin ilmi, ko mai son ilmi, kada ka kasance na biyar sai ka halaka[7].

c- Mahankalta

241. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Ba komai gareka ka yi abota da ma’abocin hankali, koda kuwa ba ka godewa kyautarsa ba, sai dai ka amfana daga hankalinsa, ka guji munanan halayensa, kada ka bar abota da mai karimci koda kuma ba ka amfana daga hankalinsa ba, to sai ka amfana da karimcinsa da hankalinka, ka gujewa dukkan mai rowa wawa[8].

d- Masu Nasiha

Kur'ani:

“Sai ya juya gabarinsu kuma ya ce: ya ku mutane hakika na isar muku da sakon Ubangijina, kuma na yi muku nasiha, sai dai ku ba kwa son masu nasiha”[9].

Hadisai:

242. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Babu alheri ga mutanen da ba masu nasiha ba ne, kuma ba sa son masu nasiha[10].

243. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mutum mai tausayi mai nasiha ya kasance shi ne; mafi soyuwar mutane gunka[11].

e- Mutane Nagari

244. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: son mutum nagari ga nagari lada ne ga nagari, son fajirai ga nagari falala ce ga nagari, kin fajirai ga nagari ado ne ga nagari, kin nagari ga fajirai kaskanci ne ga fajirai[12].

245. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ya kai mai neman ilmi, hakika ilmi yana da falala mai yawa, kansa shi ne kaskan da kai, kuma jagoransa shi ne shiriya, abokinsa kuwa shi ne son zababbun mutane nagari[13].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next