Hukunce-hukuncen Soyayya



256. Daga Abu Ya’ala daga Anas dan Malik: Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mafi tausayi ga yara. Ya kasance yana da wani da mai shan nono a wata nahiyar garin Madina, kuma ya kasance akwai wata mata mai shayar da shi, ya kasance yana zuwa wurinsa tare da mu, kuma ya yi wa gidan hayaki da turare mai kanshi, sai Annabi ya shaki kanshinsa (yaron), sannan ya sumbance shi, sannan sai ya koma[24].

l- Da

257. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Allah yakan tausaya wa bawa saboda tsananin sonsa ga dansa[25].

258. Sahihul buhari, daga Abu huraira ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya sumbanci Hasan dan Ali kuma a wurin akwai al’akar’u dan habis attamimi yana zaune, sai al’akara’u ya ce: ni hakika ina da’ya’ya goma, amma ban taba sumbutar wani daga cikinsu ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya kalle shi sannan ya ce: Duk wanda ba ya tausayawa to ba a tausaya masa[26].

m- Makoci

259. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce wa Dawud dan sarhan: Ya kai Dawud hakika kyawawan halaye wasunsu an dabaibaye su da wasu ne, Allah yana raba su yadda ya so… da kuma kauna ga makoci da aboki[27].

n- Mai Ladabi

260. Rijalul kashi, daga ibn abi umair: Abu Abdullahi (A.S) ya kasance idan ya yi duba zuwa ga Fudhail dan yassar yana zuwa sai ya ce da shi: “ka yi albishir ga masu kaskanda kai”[28], ya kasance yana cewa: Hakika fudhail yana daga sahabban babana, kuma ni ina son mutum ya so abokan babansa[29].

o- Wanda Ba Ya Kinka

261. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: yana da kyau ka so wanda ba ya kin ka[30].

262. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Wanda duk ka amita daga cutar da shi, to ka kwadaitu da ‘yan’uwantakarsa[31].

P- Wanda Amfaninsa Gareka Ne,Cutarwarsa Ga Waninka

263. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: yana da kyau ka so wanda amfaninsa yake gareka, kuma cutarwarsa take ga waninka[32].

7 / 3

Wanda Sonsa Ya Haramta

a- Makiya Allah

Kur'ani:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next