Hukunce-hukuncen Soyayya



266. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: game da fadin Allah madaukaki: “Kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku” shi ne mutum ya zo wa sarki sai ya so wanzuwarsa har sai (sarki) ya sanya hannunsa aljihunsa sai ya ba shi (wani abu na duniya)[40].

c- Wanda Ya Ki Wasu Jama’ar Musulmi

267. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk wanda ya ki wasu daga al’ummar musulmi to ya wajaba musulmi su yi gibarsa, kuma adalcinsa ya saraya daga tsakaninsu, kuma ya wajaba a kaurace masa[41].

7 / 4

Wanda ake kin sonsa

a- Ashararai

268. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: abota da ashararai tana jawo sharri, kamar iska ce da take wuce mushe tana daukar wari[42].

269. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mai zama da ahsrarai kamar mai hawan kogi ne; idan ma bai nutse ba, to ba ya aminta daga tsoro[43].

270. Daga Imam Muhammad Jawad (A.S) ya ce: na hana ka abota da ashararai, hakika shi asharari kamar takobi ne da ka zare; kallonsa yana kayatarwa amma saransa yana muni[44].

b- Fasiki

271. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ‘yan’uwantakar fajirai tana daga mafi girman wauta[45].

272. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka kiyayi abota da faskikai da fajirai, da kuma masu bayyanar da sabon Allah [46].

c- Makaryaci

273. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka nisanci abota da makaryaci, domin idan ka bukace shi sai ya zamanto ba ka gaskata shi, kuma kai ba ka gaya masa cewa kai kana karyata shi, ga shi yana fita daga zuciyarka kuma shi ba ya barin dabi’arsa[47].

d- Mahassada

274. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mai hassada yana bayyanar da sonsa a cikin maganganunsa, kuma yana boye kiyayyarsa a cikin ayyukansa, yana da sunan aboki da kuma siffar makiyi[48].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next