Hukunce-hukuncen Soyayya



“Ya ku wadanda kuka yi imani kada ku riki makiyina kuma makiyinku masoya, kuna nuna musu kauna alhalin hakika sun kafirce da abin da ya zo muku na gaskiya, suna fitar da manzo da ku (daga garinku) don kun yi imani da Allah Ubangijinku idan kun kasance kun fito yaki ne a tafarkina, da kuma neman yardata kuna sirranta musu kauna, alhalin ni na san abin da kuka boye da abin da kuka bayyanar, kuma duk wanda ya yi haka daga cikinku to hakika ya bacewa tafarkin katari” [33].

“Ba zaka taba samun mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira suna kauna ga wanda ya keta (dokokin) Allah da manzonsa ba koda kuwa sun kasance iyayensu ne, ko ‘ya’yansu, ko kuma ‘yan’uwansu, ko jama’arsu, wadannan (su ne wadanda) Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu kuma ya karfafe su da ruhi daga gareshi, kuma ya shigar da su aljanna da koramai suke gudana ta karkashinta, suna masu dawwama a cikinta Allah ya yarda da su kuma su ma sun yarda da shi, wadannan su ne rundunar Allah, ku sani hakika rundunar Allah su ne masu rabauta” [34].

“Ya ku muminai kada ku riki abokan sirri daga waninku su kuma ba sa sassauta muku kiyayya, kuma suna gurin abin da zai wahalar da ku, kuma hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu, kuma abin da kirazansu (zukatansu) suke bayyanarwa ya fi muni, hakika mun bayyanar muku da ayoyi idan kun kasance masu hankali. Ku ne wadanda kuke kaunarsu amma su ba sa kaunarku, kuma kuna imani da littafi gaba dayansa, idan suka hadu da ku sai su ce mun yi imani, idan suka wuce sai su ciji yatsu saboda takaici, ka ce; ku mutu da takaicinku, hakika Allah ne masani da ma’abota kiraza (zukata) [35].

“Kada mumunai su sake su riki kafirai masoya ba muminai ba, duk wanda ya yi hakan ba komai ba ne shi a wajen Allah, sai dai idan kun ji tsoro daga garesu (to sai ku boye imaninku) kuma Allah yana yi muku gargadin ku ji tsoronsa, kuma zuwa ga Allah ne makoma take” [36].

Hadisai:

264. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya yi ‘yan’uwantaka da kafiri, kuma kada ya cakuda da fajiri, domin wanda ya yi ‘yan’uwantaka da kafiri ko ya yi cakuda da fajiri zai kasance kafiri fajiri[37].

265. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: yi hattara da son makiya Allah, ko kuma ka bayar da kaunarka ga wasun masoya Allah; domin duk wanda ya so mutane za a tashe shi tare da su[38].

b- Azzalumai

Littafi:

“Kada ku karkata zuwa ga azzaluimai sai wuta ta shafe ku sannan ba ku da wasu masoya sabanin Allah, sannan kuma ba za a taimake ku ba” [39].

Hadisai:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next