Hukunce-hukuncen SoyayyaHukunce-hukuncen Soyayya
7 / 1 Wanda Sonsa Yake Wajibi Ne
Kur'ani: “Ka ce idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku da matanku da ja’amarku da dukiyoyi da kuka tara ta, da kasuwanci da kuke jin tsoron tasgaronsa, da gidaje da kuke yarda da su, sun fi soyuwa zuwa gareku fiye da Allah da manzonsa da yaki a tafarkinsa, to ku saurara har sai Allah ya zo da lamarinsa, kuma Allah ba ya shiriyar mutane fasikai†[1]. “Ka ce ni ba na tambayarku wani lada a kansa sai dai kauna ga ma’abota kusanci†[2]. Haidsai: 236. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Bawa ba zai taba imani ba har sai na kasance mafi soyuwa zuwa gareshi daga kansa, kuma iyalina sun fi soyuwa zuwa gareshi fiye da iyalina, kuma kaina ta fi soyuwa zuwa gareshi fiye da kansa[3]. 237. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Asasin mulunci shi ne sona da son ahlin gidana[4]. 238. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: sonmu mu Ahlul Baiti (A.S) shi ne tsarin addini[5]. 7 / 2
|