Sabuban SoyayyaK- Neman tsarin Allah
102. Imam zainul abidin (A.S): Ubangiji ka sanya soyayyata a zukatan bayinka… kada ka sanya mu daga gafalallu, ka so ni, ka sanya sona, ka soyar da ni abin da kake so na zance da aiki; har sai na shiga cikinsa da jin dadi[62]. 103. Littafin manla yahadhuruhul fakih: ya kasance daga wasiyyar Manzon Allah (S.A.W) ga Ali (A.S): ya Ali, idan ka nufi wani birni ko wata alkarya yayin da ka ganta ka ce: ya Ubangiji ni ina rokon ka alherinta, ina kuma neman tsarinka daga sharrinta, ya Ubangiji ka soyar da mu gun ahlinta, kuma ka sanya son salihan ahalinta garemu kuma [63]. 3 / 6 Abin Da Yake Wanzar Da Kauna
Kur'ani: “Masoya a wannan rana sashensu makiya ne ga sashe, sai dai masu takawaâ€[64]. Hadisai: 104. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ‘yan’uwa saboda Allah madaukaki soyayyarsu tana dawwama; saboda dawwamar sababinta[65]. 105. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Son ‘yan duniya yana yankewa; saboda sababinsa yana yankewa. Son ‘yan lahira yana dawwama; saboda dawwamar sababinsa[66]. 106. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kyakkyawan zama yana dawwamar da kauna[67]. 107. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Ka tausasa tafinka; domin duk wanda ya tausasa tafinsa to zai dawwamar wa mutanensa soyayyarsa[68].
|