Sabuban SoyayyaSabuban Soyayya
1 / 3 Ilhama
Kur'ani: “Muka sanya kaunar juna da rahama a tsakaninkuâ€[1]. “Na jefa maka soyayya da kauna daga gareni, domin a rene ka a kan idanuna (bisa kariyata)â€[2]. Hadisai: 47. Imam Ali (A.S) ya ce da wani bayahude da ya ce masa: hakika Allah ya jefa wa Musa dan imrana (A.S) soyayya daga gareshi: ya ce: haka ne, kuma an ba wa Muhammad (S.A.W) sama da hakan, hakika Allah ya jefa masa soyayya daga gareshi, wane ne ya yi tarayya da shi a wannan suna, yayin da Allah madaukaki ya cika shahada da shi, shahada ba ta cika sai dai fadin cewa: na shaida babu wani abin bauta sai Allah, kuma na shaida cewa Muhammad manzon Allah neâ€. ana shelanta hakan a kan mimbari, ba a daga wani sauti da ambaton Allah sai an daga ambaton Muhammad (S.A.W) tare da shi[3]. 48. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ga wadannan da suke sauraron bayyanar Imam mahadi (A.S): amma kuna son Allah ya bayyanar da gaskiya da adalci a bayan kasa, ya kuma hada kalmar musulmi waje daya, ya kuma hada tsakanin zukata mabambanta?![4] 2 / 3 HaduwarRayuwaka
49. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: rayuka jama’a ce ababan Tarawa, wadanda suka san juna sai su hadu, wadanda suka ki jituwa sai su saba[5]. 50. Imam Ali (A.S) ya ce: rayuka iri-iri ne, duk wanda suka daidaitu sai su shaku, mutane sun fi karkata ga irinsu[6].
|